
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙasar Portugal ta yi nasarar lashe kofin gasar UEFA Nations League a karo na biyu biyu bayan doke Sifaniya da ta yi a bugun fenareti a Birnin Munich.
Ɗan wasa Ruben Neves ne wanda ya zura ƙwallon da ya bai wa Portugal nasara, lamarin da ya sanya Ronaldo kukan murna bayan da aka tashi wasan a 2 da 2.
Ɗan wasan da Arsenal ta ke hari, Martin Zubimendi shi ya fara zura ƙwallon da ya bai wa Sifaniya dama a karon fari, kana daga bisani bayan minti biyar Nuno Mendes na Portugal ya farke.
Mikel Oyarzabal, wanda ya zura ƙwallon da ya bai wa Sifaniya nasara a wasan ƙarshe na gasar Euro 2024, ya ci ƙwallo na biyu, wanda Cristiano Ronaldo ya farke a minti na 60.
An tashi a bugun daga kai sai mai tsaron gida Portugal ta yi nasara da ci 5 da 3.
