Daga USMAN KAROFI
Tsohon shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (Rtd), yana cikin ƙoshin lafiya a Abuja kuma ya yi bikin Sallah cikin kwanciyar hankali tare da iyali da abokai. Wannan na zuwa ne bayan rahotannin ƙarya da suka yaɗu a kafafen sada zumunta na cewa an kai masa hari. Hadiminsa, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman (Rtd), ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.
Usman ya ƙaryata rahoton da wasu kafafen yanar gizo suka wallafa, yana mai cewa hakan “ba gaskiya ba ne kwata-kwata” kuma ƙarya ce da marasa kishin ƙasa suka ƙirƙira domin tayar da hankali da ruɗani. Ya ce Buratai wanda tsohon jakadan Najeriya ne a ƙasar Benin, bai fuskanci wani hari ba, kuma yana ci gaba da zama a cikin babban birnin tarayya lafiya lau.
Hadimin ya ƙara da cewa sun yaba da irin goyon baya da damuwa da ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa suka nuna, yana mai kira da a dakatar da yaɗa labaran ƙarya. Ya ce duk wani yunƙuri na ɓata sunan Buratai ba zai yi nasara ba, domin gaskiya za ta ci gaba da bayyana, kuma tsohon shugaban sojin ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare Najeriya.
