Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Nijeriya reshen jihar Benuwai ta koka kan tursasawa, satar shanu da barazana ga rayuwar mambobin ta a wasu yankunan jihar.
Ƙungiyar ta yi alhinin kashe ɗaya daga cikin mambobinta mai suna Sanni Hassan, wanda ta ce wasu da ake zargin matasa ‘yan ƙabilar Tibi ne suka kashe shi a North Bank da ke Makurdi a makon jiya.
Shugabannin ƙungiyar a jihar, Ardo Risku da Ibrahim Galma da sakatare ne suka bayyana hakan a wata sanarwa da suka rabawa manema labarai a Makurdi, ranar Lahadi.
Har ila yau, sun yi zargin cewa an sace shanu 1,185 a tsakanin 15 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni, a ƙananan hukumomin Agatu da Guma na jihar, inda suka ce ‘yan sanda sun ƙwato 162.
Ana ci gaba da samun zaman ɗar-ɗar a jihar biyo bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da kai hare-hare a kan al’ummomi.
Mazauna yankin sun gudanar da zanga-zanga, inda suka zargi makiyaya da haddasa ɓarna tare da kashe mutanensu.
Sai dai a wata sanarwa da makiyayan suka fitar a ranar Lahadin da ta gabata, sun yi ikirarin cewa ana tursasa su da kuma tsoratar da su a jihar, ciki har da sace musu shanu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A tsakiyar watan Mayun 2025, an sace shanu 150 na Umar Rabiu da wasu shanu 130 na wani makiyayi a ƙaramar hukumar Agatu ta jihar Benuwai.
“Kwanan nan, adadin shanu 905 da tumaki 54 na Abubakar Abdullahi, Babangida Hassan, Samaila Baba da Sanni Hassan, an sace su ne a ranar 2 ga watan Yuni, 2025, kusa da yankin Yogbo da ke ƙaramar hukumar Guma ta jihar Binuwai.
“Rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai ta kama ɓarayin tare da ƙwato shanu 162, daga cikinsu 33 sun samu raunuka, inda shanu 743 da tumaki 54 suka rasa rayukansu.
Ƙungiyar ta yi nadamar cewa a yayin da masu shanun suka yi tattaki zuwa Makurdi don neman waɗanda ‘yan sanda suka ƙwato a ranar Talata, “wasu matasa da ake zargin ‘yan ƙabilar Tibi ne suka kai musu hari a kan babbar hanyar da ke kusa da garejin Lafiya a cikin yankin North Bank, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Sanni Hassan.
Makiyayan sun yi kira ga gwamnati da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar da su gudanar da bincike tare da kama waɗanda suka kashe mambobinsu da ɓarayin shanun su.
Sun kuma nemi goyon bayan gwamnati ga mambobinsu da aka sace musu shanu da kuma iyalan waɗanda suka rasu.
Da aka tuntubi shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Melɓin James, ya bayyana cewa ya samu rahoton, inda ya ƙara da cewa tuni jami’an tsaro na gudanar da bincike kan lamarin.
Ya yi kira da a yi haƙuri a ɓangaren ƙungiyar har sai an kammala bincike.
Ya ce, “Mun samu irin waɗannan rahotanni kuma ‘yan sanda suna kan binciken lamarin, ina kira ga hukumar MACBAN da ta yi haƙuri har sai an kammala binciken ‘yan sanda,” inji shi.
Kazalika, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da kashe wani ɗan ƙungiyar tare da ƙwato wasu shanu, amma ba ta bayar da adadin shanun da aka sace da aka ƙwato ba.
Ta ce, “Gaskiya ne, rundunar ta ƙwato wasu shanu daga hannun ɓarayin kuma an kashe wani ɗan ƙungiyar a North Bank.”
Rundunar ‘yan sandan ta gargaɗi masu aikata laifuka da su daina satar shanu domin kwantar da tarzoma a jihar.
