
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Amurka a ƙarƙashin jagorancin Donald Trump na shirin ƙaddamar da haramta shigar ƙasar ga ƴan Nijeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa, wata takarda daga Sakataren Gwamnatin Marco Rubio, ta ƙunshi gabatar da buƙatar taƙaice bada biza ko shigar ƙasar akan ƙasashe guda 36, waɗanda galibinsu na Afirka ne har da Nijeriya.
An buƙaci ƙasashen su cike ƙa’idodin da aka gindaya nan da kwanaki 60 ko kuma su fuskanci takunkumin shiga ƙasar.
Ƙasashen sun haɗa da: Angola, Benin, Burkina Faso, Cabo Verde, Kamaru, Côte d’Ivoire, Jamhuriyar Dimukraɗiyyar Kongo, Djibouti, Habasha, Misra, Gabon, Gambia, Ghana, Liberia, Malawi, Mauritania, Nijar, Nijeriya, São Tomé da Príncipe, Senegal, Sudan Ta Kudu, Tanzania, Uganda, Zambia, da kuma Zimbabwe.
Sauran sun haɗa da Antigua and Barbuda, Dominica, Saint Kitts da Nevis, Saint Lucia, Bhutan, Cambodia, Kyrgyzstan, Siriya, Tonga, Tuvalu, da Vanuatu.
A watan Maris ne Trump ya sanya takunkumin shiga Amurka ga ƙasashe 43, waɗanda suka gaza bin wasu dokoki da ƙasar ta tsara.
