MURIC ta yi tir da matakin wani sarki na barazanar hana yin Musulunci a garinsa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC), ta Allah-wadai da matakin Sarkin yankin Oke Agbe a Jihar Ondo na cin Musulmi tara, tare da barazanar koran su da kuma haramta yin addinin Musulunci a garinsa bayan da wasu dodanni suka kai hari a wani masallaci da gidan limami.

An samu rahoton cewa, wasu dodanni sun kai hari a masallaci da gidan wani limami, suka lakaɗa wa matansa da ’ya’yansa duka a yankin Oke Agbe, da ke shiyyar Akoko a ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa a Jihar Ondo Jihar Ondo.

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Ishaƙ Akintola, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, dodannin sun kai wannan harin ne a ranar Alhamis 12 ga watan Yuni, nan da muke ciki.

Ya ce, “Basaraken yankin ya yi Musulmin tara da aka ci zalinsu tara, saboda sun yi ihu tare da zagin dodannin, maimakon su riƙa yin kuka suna roƙon dodannin.

“Basaraken ya umarci matan limamin su biya tarar awaki tara da tumaki bakwai da kuma ƙwarya biyu na hoto, cikin kwana uku, kafin ranar Litinin da ta gabata, ko kuma a haramta musu zama a garin.”

Farfesa Ishaƙ Akintola, ya bayyana harin a matsayin wata shaida da ke nuna yadda ake tsananin cin zarafin Musulmi a yankin Yarabawa, don haka ya kira da a ɗauki matakin shari’a a kan duk masu hannu a wannan aika-aika.

Ya ci gaba da cewa, abin da ya faru ya ƙara girman fargabar da ƙungiyar take da shi gane da makomar al’ummar Musulmi a yankin Kudu maso yammacin Nujeriya, “saboda abin sai ƙara muni yake ta yi.”

“Don haka muna Allah-wadai da wannan hari na jahiliyya, da kuma zaluncin wannan sarki, wanda ya ci karo da kundin tsarin mulkin ƙasa, a ƙarƙashin tsarin dimokuraɗiyya a ƙarni na 21.

“Muna kira da a yi wa waɗannan Musulmi adalci, kuma muna kira ga Gwamnatin Jihar Ondo ya taka wa Sarkin Oke Agbe Akoko bukri, tare da tabbatar da cewa wani abin ƙi bai samu limamin ko ’ya’yansa ko matansa ba. Sa’annan dole a janye maganar haramta musu zama a garin,” inji ƙungiyar Musulmin.

By ukarofi