Gwamnonin PDP za su gana da INEC kan rikicin kwamitin majalisar zartarwar jam’iyyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP ke cigaba da ta’azzara da rikicin muƙamin sakatare na ƙasa da na zaman kwamitin majalisar zartarwarta, gwamnonin jam’iyyar za su gana da Hukumar zaɓe (INEC) a Abuja, ranar Talata.

A sanarwar da INEC ta fitar ta hannun Sakatarenta na riƙon ƙwarya, Halliru Aminu, za a gudanar da zaman ne a yau da misalin ƙarfe 2 na rana, a ɗakin taro na hukumar zaɓen.

Majiya daga jam’iyyar da dama sun bayyana cewa, a yayin taron ne za a tattauna akan batun muƙamin Sakataren.

Haka kuma, gwamnoni da sauran jagororin jam’iyyar za su yi aikin shawo kan matsalar da ke haddasa tsaiko ga zaman majalisar zartarwar karo na 100 da ta ke shirin gudanarwa.

Tun da PDP ta yi rashin nasara a zaɓen 2015 ta ke fama da matsalolin rikici tsakanin ƴaƴanta da matsalolin gudanar da taruka, lamarin da ya sa wasu daga ciki suke ficewa zuwa wasu jam’iyyun adawa.

By Babaji