Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa jagora ne da ya nuna kyakkyawan misali wajen yin hidima ga alhazai a matsayinsa na Amirul Hajji na jihar Kano a aikin hajjin bana.
Alhaji Muhammad Hussain Mashkur Gwangwazo ɗan kasuwa a jihar Kano kuma hadimin Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai, ya ƙara da cewa tafiyarsa aikin hajji ya baiwa shugabanni misali a matsayinsa na lamba ɗaya ya cire rigar mulki ya shiga cikin ma’aikata yana yi wa alhazai hidima.
Ya ce yadda Gwamnan Kano ya shiga ana aiki da shi domin ya tabbatar ana yin abu na inganci da kyautata jin daɗin alhazai yadda ya kamata, kuma komai ya tafi daidai don haka Gwamnan ya cancanci a jinjina masa kan wannan kyakkyawan aiki da yi masa addu’a Allah ya taimake shi ya cigaba da ba shi nasara.
Alhaji Muhammad ɗankwairo ya yi nuni da cewa daga abinda ya bashi sha’awa shine yadda Gwamna yake yin hidima da kansa ga alhazan jihar Kano ya shiga cikin masu aikin abinci ake yi da shi babu jin cewa shi Gwamna ne, ƙoƙarinsa yaya za a kyautatawa waɗanda suka je aikin Hajji.
Ya ce sannan kuma ya bada tallafin kuɗi na Riyal 100 ga kowane Alhaji na jihar Kano wanda kowanne sai da ya samu abinda in aka kwatanta da Naira an bashi N125,000 wannan ba ƙaramin abin alkhari ba ne da Alhazai suka ji daɗinsa. Ya kamata masu mulki ko muƙarraban Gwamnati da aka zaɓa su jagoranci Alhazai a ƙasar nan su yi koyi da irin wannan kyakkyawan misali da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna a aikace.
Alhaji Muhammad Hussain ya ce cikar Gwamna Abba Kabir Yusuf shekara biyu akan mulki tun daga rantsar da shi sun gamsu sosai da yadda yake tafiyar da ayyuka, domin ya zo ya yi abinda ɓwamnatin baya da ta shekara takwas bat a yi ba, ya cancanci yabo da jinjina.
Ya ce ayyukan da Gwamna yake ya nuna a zahiri shi mutum ne mai jinƙai, tausayi da faɗa da cikawa, domin irin tausayinsa ta sa wata rana da ya fita yana zaga Kano da dare ya samu wasu ‘yan ƙananan yara a rumfar filin sukuwa suna barci ƙarfe ɗaya zuwa biyu na dare, ya sa aka taho da yaran gidan gwamnati aka nemo iyayensu ya tallafa musu ya sa aka mayar da su makarantu.
Ya ce a zuwansa saboda tausayi ya tsamo ‘yan fansho da aka hana su haƙƙoƙinsu a gwamnatin baya ya zo ya biya su, akwai wata mata maƙociyarsa Hajiya Salamatu da aka biya ta fansho, kullum ce masa take ya gaishe mata da Gwamna saboda jin daɗin ya cece su, addu’a take masa Allah ya yi masa abinda ya ke buƙata.
Alhaji Muhammad Hussain Mashkur ɗankwairo ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da cewa sun ga misali na irin ɗinbin ayyuka da Gwamna yake gudanarwa a ko’ina a sassan jihar Kano, kuma an ce daga na gaba ake ganin zurfin ruwa, don haka ba sai an ce ga abinda za suyi ba, illa shawara da zai ba su shine su ƙarkaɗe ƙuri’unsu su ajiye shi har Allah ya kawo mu zaɓen 2027 a sake kaɗa ƙuri’a ga Injiniya Abba Kabir Yusuf a karo na biyu.
