Ranar yaƙi da miyagun ƙwayoyi: NDLEA a Nasarawa ta bi sahun takwarorinta na duniya don isar da saƙo

Spread the love

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya

A yayin da duniya baki ɗaya ke ci gaba da bikin ranar yaƙi da sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi na bana wato shekarar 2025 da ake ciki wato United Nations International Day Against Drug Abuse And Illicit Trafficking a Turance fannin hukumar ta NDLEA ɗin a jihar Nasarawa ta bi sahun takwarorin nata a duniya bakiɗaya inda ita ma ta gudanar da taron a birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar a mako da ake ciki.

A jawabin kwamandan hukumar a wajen babban taron, Dechi Elisha Daɓid ya bayyana cewa taken taron na bana shine “Bambancin a bayyana yake, a saka jari a fannin kiyayewa’ wato the eɓidence is clear, inɓest in preɓention a Turance ya jaddada mahimmancin ranar inda ya ce rana ce da ake yin waiwaye adon tafiya don auna ire-iren cigaba da kuma kalubalai da ake samu a fannin na yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyin a duniya baki daya tareda nemo mafita.

Ya jinjina wa shugabancin hukumar na NDLEA din na kasa baki daya karkashin jagorancin Janar Mohammed Buba Marwa dangane da sadaukarwa da kuma aiki tukuru da yake yi don tabbatar an yake wadannan mugayen ɗabi’u na sha da kuma fataucin muggan ƙwayoyin a ƙasa baki ɗaya inda yace tabbar tsare-tsaren sa da fannonin hukumar a duka jihohi ke yin koyi suna cigaba da haifar da ɗa mai ido kawo yanzu.

Dechi Elisha Daɓid ya kuma yaba wa jami’ar hukumar a jihar a duka matakai dangane da kokari da suke yi tare da haɗin kan wasu hukumomin tsaron a jihar ta Nasarawa wajen rage ko kawo ƙarshen harkar shaye-shaye da kuma fataucin muggan kwayoyin inda ya bukace su su cigaba da hakan.

Kwamandan ya kuma yi amfani da damar inda ya jaddada cewa akokari da hukumar tasu ta NDLEA a jihar keyi a fannin kawo yanzu a wata daya gabata kacal ta cimma dinbin nasarori a jihar da suka haɗa da ƙwato sama da kilogram 4,764.893 na muggan ƙwayoyi a jihar kana ta yi wasu dinbin kame-kamen masu aikata laifin da dama da sauran su tare da bayyana cewa ta turo da dama kotu tareda bai wa saura shawarwari da zasu taimaka wa rayuwan su da sauran su ta wani shirin hukumar na musamman da ake kira WADA a turance.

Sauran manyan baƙi da suka gabatar da nasu jawabi a wajen taron duk sun yaba wa namijin kokari da hukumar keyi a jihar don yakan miyagun mutanen dake harkar ta sha da kuma fataucin muggan kwayoyin kana sun bukace Hukumar kada suyi kasa a gwiwa su cigaba da hakan.

Abubuwan da aka gudanar a yayin mahimmin taron na bana sun hada da gudanar da wasu dirama na musamman daga ‘yan makarantun sakandare dabandaban a jihar da ‘yan hidimar ƙasa wato NYSC dake idar da sakonnin munanan illolin sha da fataucin miyagun kwayoyin a rayuwar ɗan adam da sauran su.

By ukarofi