Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta yi gargaɗi ga sarakunan gargajiya a jihar Ondo, inda ta buƙace su da su daina ba da haya ko sayar da filaye ga masu noman tabar wiwi.
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan kama wasu mutane 294 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi muggan ƙwayoyi a tsakiyar shekarar 2025.
Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Akure, kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, Mista Nanzing Daniel Salah, ya bayyana cewa an gano wasu gonakin tabar wiwi da dama a cikin dazuzzukan mallakin cibiyoyin gargajiya.
Salah ya yi tsokaci kan alaƙar noman miyagun ƙwayoyi da kuma ƙaruwar rashin tsaro, inda ya ce ana amfani da kuɗaɗen da ake samu daga waɗannan gonakin wajen gudanar da ayyukan ta’addanci. Ya kuma yi tir da illar da noman tabar wiwi ke haifarwa a muhalli, wanda a cewarsa yana lalata dazuzzukan jihar tare da rage wadatar filayen noman abinci.
“Dole ne cibiyoyin gargajiya su daina sayar da filaye ga masu noman ƙwayoyi,” inji shi.
“Wadannan filaye, waɗanda galibi suna cikin dazuzzuka, ana amfani da su ne wajen noman wiwi, kuma kuɗaɗen da ake samu daga wannan sana’ar na haifar da laifuffuka daban-daban, mafi muni kuma, irin waɗannan ayyuka na lalata albarkatun ƙasa da kuma haifar da ƙarancin abinci ta hanyar ƙwace filayen noma daga noman abinci.”
Kwamandan hukumar ta NDLEA ya bayyana cewa, a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni 2025, hukumar da ke aiki tare da sauran jami’an tsaro, sun lalata gonakin tabar wiwi sama da hekta 29,656, tare da kwace kusan kilogiram 22,710.6 na haramtattun abubuwa.
Salah ya bayyana damuwarsa kan abin da ya bayyana a matsayin haɗakar wasu al’ummar yankin, inda ya zarge su da kare masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma kawo cikas ga ƙoƙarin hukumar ta hanyar ɓoye bayanan sirri.
Duk da waɗannan ƙalubalen, hukumar ta NDLEA a cewarsa, ta samu gagarumin ci gaba, inda aka gyara masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi 130, an kuma yanke wa mutane 33 da ake zargi da laifi hukunci, sannan an ƙwace motoci biyar.
Hukumar ta NDLEA na ci gaba da ƙara ƙaimi a faɗin jihar Ondo da sauran jihohin ƙasar wajen yaƙar noma, cin zarafi, da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da yin kira ga cibiyoyin gargajiya da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma da su taka rawar gani a wannan yaƙi.
