Daga UNCLE LARABI
Tinubu ya gana wa ’yan Nijeriya azabar gashin aya ko gyaɗa a hannu. A mulkin Tinubu ne kuɗin kaza ya koma na akuya da tinkiya. A mulkin Tinubu ne kuɗin tinkiya da akuya ya koma kuɗin saniya. A mulkin Tinubu ne kuɗin rago ya koma kuɗin bijimin sa ko ƙaton raƙumi. A mulkin Tinubu ne kuɗin sa da raƙumi suka koma kuɗin gida da mota da hajji da kuɗin auren kyawawan ‘yammata guda biyu lokaci ɗaya. Kuɗin kujerar aikin Hajji Naira miliyan 8.5, wanda kafin zuwansa sai mutum uku su je Hajji da wannan kuɗin.
Kar Allah ya maimaita mana mulkin Tinubu ɗin nan. Allah ya sa daga wannan zango ya faɗi a zaɓe, wani mai adalcin ya ci zaɓen.
Allah ya dubi talakawan Nijeriya ya aiko mana da wanda zai samar mana da adalci da jin daɗi a ƙasar bakiɗaya ta yadda wutar lantarki za ta inganta, ruwa zai samu, asibitocin gwamnati su gyaru, hanyoyin sufuri na ƙasa su gyaru, wato tituna, makarantun gwamnati su gyaru su koma kamar da ana samun ilimi mai Inganci, talaka ya samu ya dinga cin ƙwai yana shan madara a shayi, ya ci nama ko kifi a miya, idan ya yi nishaɗi ya yanka kaza ya ci abinsa.
Allah ya kawo mana zaman lafiya da tsaro a kasarmu Nijeriya!
Uncle Labari marubuci ne a Kano
