Mayaƙan Lakurawa sun halaka ƴan sanda uku a Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani yunƙuri na yin garkuwa da mutane a hanyar Zogirma zuwa Tilli dake Ƙaramar Hukumar Bunza ta Jihar Kebbi, mayaƙan ƙungiyar Lakurawa sun kashe jami’an ƴan sanda guda uku.

Lamarin ya auku ne a lokacin da rundunar ƴan sanda a Zogirma ta samu labarin harin ƴan ta’addar, inda cikin hanzari ta tura jami’ai zuwa yankin tare da ƙarin dakaru daga babban ofishinsu dake Birnin Kebbi.

Bayan musayar wuta da aka yi tsakanin ɓangarori biyun ne, ƴan sanda uku suka rasa rayukansu.

A sanarwar da Kakakin ƴan sandan jihar, Nafi’u Abubakar ya fitar, ya ce ƴan ta’adda da dama sun rasu a yayin ba-takashin.

Ya kuma ce, kwamishinan ƴan sandan jihar, Bello Sani ya yaba wa jajircewa da sadaukarwa gami da shahadar jami’an ƴan sandan.

Haka kuma, Gwamna Nasir Idris ya tabbatar harin tare da rashin jami’an da aka yi a lokacin da ya ke sanar da ɗage taron masu-ruwa-da-tsaki na jam’iyyar APC a Birnin Kebbi.

A wani labari kuma, dakarun sojoji daga ƙaramar bataliya ta 223, sun yi nasarar daƙile wani babban harin ƴan bindiga a garin Ribah dake Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a jihar.

A ranar Laraba ne al’amarin ya faru, inda ƴan bindiga sama da guda 400 ɗauke da muggan makamai suka kai harin. A yayin ba-takashi ne sojojin suka yi nasarar halaka da dama daga cikinsu.

By Babaji