Labarin ɓeraye sun addabi Fadar Shugaban Ƙasa rufa-rufa ne ga rashin lafiyar Buhari, inji Garba Shehu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Kakakin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya bayyana cewa batun ɓeraye sun addabi Fadar Shugaban ƙasa abu ne da aka ƙirƙira domin karkatar da hankulan al’umma daga matsalolin rashin lafiyar Buhari.

A littafinsa mai suna ‘According to the President: Lessons from a Presidential Spokesperson’s Experience’, Shehu ya ce ya ƙirƙiri labarin ɓerayen ne da nufin ɗauke hankulan jama’a daga batun rashin lafiyar Buhari da nazari akan ƙarfinsa na yin shugabanci.

Gabannin Buhari ya dawo Nijeriya a ranar 19 ga Agustan 2017 bayan shafe kusan watanni uku yana karɓar magani a Tarayyar Turai, Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ya yi ikirarin an maye gurbin Buhari da wani mai suan Jibrin daga Sudan.

Bayan dawowar Buhari Nijeriya ne wasu ƴan Nijeriya suka shiga kokwanto akan ko asalin Buharin ne ko kuma Jibrin na Sudan kamar yadda Kanu ya yi ikirari.

Al’amarin ya yi ƙamari ne a lokacin da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar da sanarwar cewa Buhari zai riƙa yin aiki daga gida a madadin ofishinsa dake fadar, lamarin da ya sa kokwanto akan lafiya da ƙarfin jagorancinsa ya girmama.

Garba Shehu ya ƙara da cewa, a lokacin da ƴan jaridar suka matsa don samun dalilin da ya sa Shugaban ƙasar zai yi aiki daga gida a madadin ofishinsa, sai ya faɗa musu cewa wajen yana da buƙatar gyara ne kasancewar ɓeraye sun yi wa wasu wayoyi a ofishin dameji.

By Babaji