A samar da tsaro a gonaki, don a yaƙi yunwa a Arewa

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A yayin da damina ke ƙara kankama, yanayin da manoma da sauran al’ummar ƙasa ke sa rai da samun amfanin gona mai yawa, don samar da wadatar abinci, jihohi da dama na ƙasar nan na fuskantar ƙalubalen tsaro. Rikicin manoma da makiyaya, da sace-sacen mutane don a yi garkuwa da su a karɓi kuɗi na ƙara tsananta a jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, har ma da yankin Arewa maso Gabas, inda ake fitar da ɗimbin amfanin gona, da kayan abinci iri-iri, wani lokaci ma har ana fitar da wasu zuwa ƙasashen waje.

Jihohi irin su Katsina, Zamfara, Sakkwato, Neja, Filato, Nasarawa, Binuwai da Taraba sun tsunduma cikin mummunar fitina ta rashin tsaro, sakamakon yadda mahara da ke amfani da makamai ke shiga ƙauyuka da gonaki suna kashe mutane maza da mata, da lalata amfanin gona, don mugunta da ƙeta. Waɗannan jihohi ne da ake samun albarkar ƙasar noma da fitar da abinci mai yawa, amma yanzu fita zuwa gonaki ya gagara. Mutum na fita zuwa gona sai dai a dawo da gawarsa, ko a neme shi a rasa, ko kuma a je a ga an sare amfanin gonar da ya fara fitar da yabanya mai kyau. A irin wannan lokaci da ‘yan Nijeriya ke fuskantar matsin tattalin arziƙi da tsadar abinci, mutane na kukan yunwa da rashin wadatar abinci a ƙasa. Lallai akwai abin fargaba da tsoratarwa.

Rikice-rikice na baya-bayan nan da suka haifar da asarar ɗimbin rayuka a jihohin Filato da Binuwai yana ƙara nuna yadda girman matsalar tsaro take a ƙasar nan. ƙarancin jami’an tsaro na gwamnati, ya ƙara hassala yadda ake waɗannan kashe-kashe cikin lunguna da ƙauyuka, inda babu hanyoyi masu kyau da za a iya shiga don a kai musu ɗaukin gaggawa. Abin da ya ƙara sa al’ummar yankunan cikin babbar damuwa sosai.

ƙoƙarin da wasu jihohi ke yi na kafa ƙungiyoyin ’yan banga da ake zaɓowa daga cikin al’umma ana ba su horo kan yadda za su yi amfani da makami da samar da ingantattun bayanan sirri ga jami’an tsaro, yana haifar da alheri a wasu wuraren, domin kuwa rahotanni na bayyana cewa ana samun raguwar irin waɗannan ayyukan laifi da ake yi a ƙauyuka, da ke hana zuwa gonaki don noman abinci. Yayin da a wasu wuraren gwamnati da shugabannin ’yan ta’adda ke ƙulla yarjejeniyar sulhu, don a bai wa jama’a damar zuwa gonakinsu da neman abinci.

Haƙiƙa akwai abin tausayi da firgitarwa idan mutum ya shiga cikin waɗannan ƙauyuka ya ga yadda jama’a ke rayuwa, cikin ƙangin talauci, yunwa da rashin tsaro, ba tare da, shugabannin su da wakilan da suka zaɓa sun iya yi musu wani abu a kai ba. Irin wannan yanayi ne yake sa ake ci gaba da samun sabbin masu aikata laifuka waɗanda yunwa da wahala ke tilasta musu shiga daji don samar wa kansu mafita.

Lallai wannan ƙalubale ne babba ga Gwamnatin Tarayya na ta samar da ƙarin jami’an tsaro da za a bai wa horo na musamman kan yadda za su magance matsalolin da ke addabar al’umma a cikin ƙauyuka, musamman inda ake noman abinci mai yawa. Kodayake, kafa rundunar tsaro ta Agro Rangers masu tsaron manoma a ƙauyuka, ya taimaka a wasu wuraren, amma girman matsalar ya sa basa iya sauke nauyin da aka ɗora musu. Sannan girman yankin da ake fuskantar wannan bala’i da sarƙaƙiyar dake cikin sa ya sa aikin nasu ya ƙara wahala ainun. Jami’in tsaro ɗaya ko biyu ba zai wadatar ba, a wurin da ake da gungun ’yan bindiga masu yawa da manyan makamai. Babu wani abu da za su iya yi, ko kuma duk ƙoƙarin da za su yi ba zai je ko’ina ba, zai zama kamar ba a yi komai ba.

A daidai lokacin da nake wannan rubutu, rundunar tsaro ta Civil Defence ta yaye wasu jami’an samar da tsaro a gonaki da ƙauyuka, wato agro rangers guda 150 a Jihar Filato da niyyar tallafawa ayyukan tsaro a wasu yankunan jihar. Wannan adadi ne da za a ce yayi kaɗan ainun duba da tsananin yanayin taɓarɓarewar tsaro a jihar da munin da rikicin makiyaya da manoma a jihar ke yi. Ina laifin dubu 1500, a babu-babu za a iya kasa su zuwa duka shiyyoyi uku na jihar, arewaci, tsakiya da kudanci. Babu ma kamar a ƙananan hukumomi irin su Mangu, Bokkos, da Riyom, Wase da Kanam, inda ’yan bindiga ke cin karensu babu babbaka. Duk kuwa da ƙoƙarin da jami’an tsaro na Operation Safe Haven, da sauran haɗin gwiwar rundunonin tsaro ke yi a yankin. 

Rundunar sojojin sama ta Nijeriya, a makon da ya gabata ta fitar da wani gargaɗi na musamman ga ’yan ta’adda a yankunan Zamfara da Katsina cewa su bar wuraren da suka mamaye kuma suke ayyukan ta’addanci da hana jama’a noma da walwala, yayin da take dab da fara farautarsu da jiragenta masu shiga dazuka suna yaƙi da su. Sai dai wannan gargaɗi da kai hare-hare ta sama ba zai yi maganin waɗannan ‘yan bindiga ba, in ba tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin tsaro na ’yan sakai da suka fito daga cikin yankunan ba. Dole ne a ƙara basu horo da ƙwarin gwiwa, a nuna musu dabarun yaƙi da ’yan ta’adda na zamani, ta yadda idan an koro su ta sama, su ma za su tare su ta ƙasa. Rahotanni na nuni da irin nasarori da irin wannan haɗin gwiwa ya samar, inda kafar watsa labarai ta Arise TV ta rawaito cewa, fiye da kimanin ‘yan bindiga 100 ne haɗin gwiwar ’yan sakai da ke samun goyon bayan Gwamnatin Jihar Zamfara suka hallaka a wata arangama da suka yi da wani ɓangare na yaran riƙaƙƙen ɗan bindigar nan Bello Turji. 

Kodayake, a wasu jihohin ba haka abin yake ba. A Jihar Filato ƙoƙarin ’yan sakai ya gamu da cikas sakamakon kisan da da aka ce ’yan bindiga sun yi wa wasu ’yan sakai su kimanin 70 a wani karon-batta da suka yi a ƙauyen Dutsen Zaki da ke ƙaramar Hukumar Wase, yayin da wasu 16 ke jinya a asibiti. Kodayake su ma ’yan bindigar an yi musu ɓarna sosai a faɗan da aka ce an shafe tsawon kwanaki uku ana fafatawa, amma abin takaici ne irin yadda ake samun ɓatagari dake haɗa baki da ’yan bindiga ana yi wa ’yan sakai kwaton ɓauna a wasu lunguna, da ƙauyukan da, suke ba da gudunmawa. 

Lallai ne gwamnati ta jagoranci samar da horo na musamman, ga ɗimbin matasan mu da ke neman aikin yi, cikin aikin rundunonin tsaro na ’yan sakai. Kuma a ware musu wani alawus da zai ƙarfafa musu gwiwa wajen aikin da za su yi na sadaukarwa da samar da kariya ga yankunan su da al’ummar su. Ba na goyon bayan masu cewa, jama’a su ɗauki makami su kare kansu, domin wannan shi ma a karan kansa gayyatar matsalar tsaro ce da za ta haifar da wani ƙalubalen nan gaba.

Gwamnati ce ya dace ta jagoranci ɗauka da horar da matasan da za a bai wa aikin, kuma a haɗa su aiki da jami’an tsaro, su riƙa aiki kafaɗa da kafaɗa. Kamar dai yadda muke gani yana gudana tsakanin jami’an ’yan sanda da ƙungiyoyin ’yan banga a wasu jihohin ƙasar nan.

By ukarofi