Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A shekarar 2023, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya sha alwashin korar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da wasu jiga-jigan jam’iyyar daga PDP.
Wike, wanda a lokacin shi ne gwamnan jihar Ribas, ya yi wannan alƙawarin ne a wajen ƙaddamar da aikin titi a ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas.
Wike ya ɗora laifin rashin kataɓus ɗin jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa da aka kammala a kan waɗanda ya ce sun ƙi bin kundin tsarin mulkin PDP. Ya yi alƙawarin korar su daga jam’iyyar da fara aikin sake gina ta.
Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin “kashi na biyu na yaƙin.”
A cewarsa: “Waɗannan mutanen sun bar jam’iyyar mu a shekarar 2014-2015, jam’iyyar mu ta yi rashin nasara, sun sake dawowa, jam’iyyar mu ta sake shan kaye.
“Sun ruguza jam’iyyarmu, za mu kore su daga jam’iyyarmu, ba su da rawar da za su taka a jam’iyyarmu.”
Wike ya kuma caccaki shugabancin jam’iyyar PDP bisa zargin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta da rashin bin ƙa’idojin zaɓe a lokacin da PDP suka ƙi bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Atiku ya fice daga PDP gabanin zaɓen 2027:
A halin da ake ciki, Atiku ya miƙa takardar yin murabus ɗinsa a shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 bayan amincewa da kafa jam’iyyar gamayyar ƙasa wato Alliance Democratic Congress (ADC).
An sanar da murabus ɗin ne a wata takarda mai kwanan ranar Litinin 14 ga watan Yuli 2025 zuwa ga shugaban jam’iyyar PDP reshen Jada 1 da ke ƙaramar hukumar Jada a jihar Adamawa.
Mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Abdul Rasheeth ne ya raba kwafin wasiƙar a ranar Laraba, 15 ga Yuli, 2025.
