Magajin Garin Landan ya ziyarci Legas don ƙarfafa alaƙar tattalin arziki da Afirka a fannin al’adu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Magajin garin Landan, Sadiƙ Khan, ya ziyarci Legas a wani ɓangare na ziyarar al’adu da nufin ƙarfafa dangantaka tsakanin sassan al’adu da ƙere-ƙere na Burtaniya da Nijeriya.

Khan ya tabbatar da kasancewarsa a Nujeriya a ranar Talata ta hanyar rubuce-rubucen da aka yi a shafukan sa na sada zumunta, inda ya saka hotuna da dama na kansa a wasu muhimman wurare a Legas, ciki har da wanda ya ke tsaye kusa da wani bango mai rubutu “Wannan Legas ce.”

A cikin saƙon nasa, Khan ya ce, “Wannan ita ce Legas: cibiyar tattalin arzikin Afirka kuma babban birnin al’adu. Daga bunƙasuwar farawa zuwa kasuwanni masu tasowa, Nollywood zuwa Afrobeats, Legas ta na samar da ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci a faɗin nahiyar. Yana da kyau na kasance a nan don ƙarfafa dangantakar kasuwanci da kuma buɗe sababbin damarmaki.”

Magajin garin Landan, wanda ke jagorantar tawagar kasuwanci ta Birtaniya, ya bayyana cewa Legas ita ce ta farko a rangaɗin birane huɗu da nufin bunƙasa kasuwanci da saka hannun jari tsakanin Burtaniya da manyan ƙasashen Afirka.

“Na ji daɗin zuwa Legas tare da wakilan mu na kasuwanci. A cikin kwanaki biyar masu zuwa, zan ziyarci birane huɗu domin inganta harkokin kasuwanci da zuba jari a cikin muhimman sassa irin su kuɗi, ilimi, kiwon lafiya, fasaha, masana’antu,” ya rubuta a cikin wani saƙon da ya wallafa.

A wani ɓangare na ayyukan sa, Khan ya halarci Legas Canvas, wani baje kolin ƙirƙire-ƙirƙire wanda Shugaban EbonyLife, Mo Abudu ya shirya, wanda aka gudanar a EbonyLife Place a Tsibirin Victoria. Taron ya tattaro manyan ’yan wasa a fannonin nishaɗi da ƙirƙira na Nujeriya, waɗanda suka haɗa da fina-finai, kiɗa, kayan sawa, da fasahar gani.

A cikin wata sanarwa da aka buga a ranar Talata a shafin yanar gizon magajin garin Landan, Khan ya bayyana cewa fannin ƙere-ƙere na Nijeriya yana ba da gudubmawar kusan dala biliyan 5.6 ga tattalin arzikin cikin gida na ƙasar.

By ukarofi