Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Wato abinda mutane da dama su ke kasa ganewa ko kuma su ke ƙin gane dalilin da ya sa aka tsani Buhari yadda bayan mutuwarsa mutane da dama ke murna, su ne
1. A tarihin siyasa a duniya, cikin shekaru 100 da su ka gabata, ba a taɓa samun wani ɗan siyasa da ya yi farin jinin talaka irin Buhari ba. Kowa shaida ne yadda aka riƙa dafifi a lokacin yaƙin neman zaɓensa. Wani ya tako daga Lagos zuwa Abuja, wani ya sha ruwan kwata, wasu sun mutu, duk saboda shi. Talakawa sun tara masa kuɗi daga aljifansu domin ya ci zaɓe, kuma ya ci zaɓen har sau biyu. Amma tsawon shekaru takwas akasarin waɗanda duk suka hidimta masa sun yarda cewa ya ci amanarsu.
Mu ɗauki jama’ar Jihar Kano, inda na fito, babu wata al’umma mai ƙuri’a da ta yi wa Buhari halarci irin Kanawa tun 2003, domin a duk kakar zaɓe su ne gaba wajen antaya masa ƙuri’a fiye da jiharsa ta Katsina. Amma me ya yi wa Kanawa na sakayya? Banda yadda ya zura ido Kano ta faɗa mummunan halin raba kan jama’arta sakamakon rikicin masarauta, wanda da a ce ya so, da ya yi maganin abin, amma sai ya rura wutar, ta hanyar goyon bayan wani ɓangare.
2. Za ka ji ana ce shi mai gaskiya ne kuma bai yi sata ba. To, wallahi gara ma a ce ya yi sata da irin yadda ya danne kan saniya aka tatse ta. A shekaru takwas na mulkinsa gwamnatinsa ta sami jumlar kuɗaɗe, tsakanin kuɗin mai da na bashi, Dala biliyan 312. Yayin da babu wani aiki ƙwaƙƙwara na Dala biliyan biyar da za a iya nunawa. Ya ci bashin da babu wata gwamnati gabaninsa da ta ci. Amma ’yan Nijeriya ba su taɓa talauci irin a lokacinsa ba yadda har aka ba mu tutar ƙasar da ta fi kowa matalauta. A ƙarƙashin Mai Gaskiya aka samu a karon farko Gwamnatin Tarayya ta siyar da mai wanda ma ba a haƙo daga ƙasa ba. Sannan mai kururuwar yaƙi da cin hanci shine wanda ya yafe wa gwamnoni biyu da kotu ta samu da laifi ta kuma ɗaure su. A lokacinsa ak zargi Emefele, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, ya yi gaba da tiriliyoyi, ‘accountant general’ ya yi gaba da biliyoyi. To, ba gara a ce shi kaɗai ma ya yi sata ba?
3. Sakamakon irin amanar da talakawa su ka ba shi, kuma ya gaza cika alƙawurrran da ya yi, ya rushe gaba, yadda ba wani ɗan siyasa a nan gaba da talakawa za su yarda da shi. Wannan illar har ta fi komai muni, domin shugabanci sai da yarda da amana kuma ya rusa ta. To, ka ga cikin illolinsa har gaba ya ciyo.
4. Buhari ya yaudari ’yan Arewa da manyan ayyuka da babu su babu dalilinsu, aikin madatsar Mambila wadda ita kaɗai sai ta canza tattalin arziki Arewa da tashar ruwa ta Baro, da haƙo man fetur a jihohin Bauchi da Gombe.
5. Har ya koma ga Allah bai taɓa nuna wa talakawa cewa ya yi nadamar halin da ya jefa su ba, wanda ya tabbatar da cewa dama ba don su ya ke neman a bashi dama ba sai, don wata buƙata ta ƙashin kansa. Allah ya ba shi dama da lafiya da sukuni har na karon mulki biyu kuma kowa ya ga yadda ya yi mulkin. Wane ‘legacy’ na cigaban al’umma ya bari?
6. Ba a taɓa samun shugaban da ya raba kan al’ummar Musulmi ba irinsa saboda janyo ’yan Izala a jiki ya kuma far wa ’yan Shi’a aka karkashe su, abinda ya daɗa rura wutar ƙiyayya ta ƙungiyanci a Arewacin Najeriya. Haka kuma ba a taɓa samun lokaci da aka sami ƙiyayya tsakanin ’yan Kudu da Arewa ba irin lokacinsa. A nan Arewa kuma ba a taɓa samun ƙiyayya tsakanin Kirista da Musulmi ba irin a lokacinsa. Ya gaji Boko Haram daga Jonathan, amma a 2019 banda Zamfara, ba wata jiha cikin rikicin tsaro a Arewa maso Yamma, amma kafin ya bar mulki jihohin Kaduna, Niger, Sokoto, Kebbi har jiharsa ta Katsina sun faɗa rikicin masu ta’addanci da garkuwa da mutane.
7. Hatta Abacha, wanda a lokacin mutuwarsa ’yan Kudu sun yi murna, amma ko Kiristan Arewa bai fito titi ya yi murna ba. Marigayi Murtala, Abacha da ’Yar’Adua duk sun mutu a mulki, amma babu wanda aka yi murnar mutuwarsa a Arewa. Me ya sa sai Buhari? Kuma duk cikin waɗannan shugabanni babu wanda ya sami rabin fari jini ko soyayyar da Buhari ya samu a Arewa.
A ƙarshe mu sani cewa, ko ka na son Buhari ko ba ka son sa, ba zai hana Allah ya tsayar masa da sikeli ba kan amanoni da Allah da jama’a suka ba shi, kuma kowannenmu zai tsaya gaban Allah, aikinka shine cetonka. Allah ba ya zalunci, kuma a tsarin adalcinsa cewa ya yi daidai da ƙwayar zarra ta hairi ko sharri za ta komo ga wanda ya aikata ta.
Ita kuma yafiya ana son ta a tarbiyar Musulunci, amma ba ta zama dole ba ga wanda aka zalunta. Ba mai yafe zalunci face wanda aka zalunta. Amma wata tarbiya ta munafinci da ke bayyana a cikinmu ita ce, da mutum ya mutu sai kowa ya yi ta ƙoƙarin wanke shi, komai zaluncin da ya aikata. Ba mai wanke wani sai Allah, kuma babu mai ɗaukar nauyin aikin wani kamar yadda Allah ya ce wato “wala taziru waziratun wizra ukhra,” duk yadda wani ya kai da sharri ba za ka ɗau zunubi guda na sharrinsa ba, haka duk alherin mutum a kansa zai tsaya. Shi ya sa Allah ya ce kowa ya yi abinda ya ga dama, (imma shakiran wa imma kafura), domin dai ya zarga mana mutuwa kuma ba mai iya kauce mata ballantana hisabinsa.
Idan ka yi da kyau, za ka ka ga da kyau, haka ma akasin hakan. A hisabin duniya dai ba don Allah ya sa Buhari ya yi wannan mulki ba, Ina kyautata zaton kabarinsa, yadda aka so shi, da ya zama hubbare irin na ɗan Fodio. Amma Shata mawaƙi ma cewa ya yi, “mu a ce mana aniyarmu ta bi mu,” domin kuwa abinda ka shuka shi za ka girba. Wanda duk yake tsoron aniyarsa ta bi shi… anya ya aikata mai kyau kuwa?
