Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamitin da gwamnatin Katsina ta kafa domin jin ra’ayoyin jama’a kan gyaran tsarin mulki ya karɓi buƙatar ƙirƙiro Jihar Karaɗua daga cikin Jihar Katsina.
Buƙatar haka na bayyane a wata takardar matsaya da gamayyar kungiyoyin haɗin kan yankin Funtua ta gabatar wa kwamitin.
Sakataren gamayyar ƙungiyoyin injiniya Tukur Lawal ya miƙa takardar ga kwamitin ƙarƙashin shugabancin Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida.
Ya bayyana cewa suna buƙatar Jihar karaɗua ne domin kawo daidaito da cigaban Najeriya domin haka ƙungiyoyin suka goyi bayan ƙirƙiro ƙarin jihar da Jihar Katsina.
Injiniya Tukur ya ce kudancin Katsina na da Ƙananan hukumomi guda 11 da suka haɗa da Funtua, Bakori, Malumfashi,kafur, Danja, kankara, Sabuwa, Dandume, Faskari Musawa da Matazu.
Ya ƙara da cewa domin cika sharuɗɗan da tsarin mulki ya tanada na kafa cikakken gudanar da mulki,suke buƙatar ƙirƙiran ƙarin Ƙananan hukumomi domin cimma daidaito wajen yawan jama’a da gudanar da aikin gwamnati.
Haka kuma sakataren gamayyar ƙungiyoyin ya ce ƙirƙiro jihar Karaɗua zai ƙara kawo jama’a kusa da gwamnati da kuma samar da ababen more rayuwa.
Gamayyar ƙungiyoyin sun kuma goyi bayan samar wa sarakunan gargajiya rawar da za su taka a tsarin mulki, musamman wajen abinda ya shafi tsaro,harkar noma da walwalan jama’a.
Sun kuma buƙaci a soke asusun bai ɗaya na ƙananan hukumomi, a cewar su tsarin mulkin Nijeriya sashi na 165(6) 1999 ya sanya karkatar da kuɗaɗe na aiwatar da ayyukan cigaban ƙananan hukumomi daga wasu gwamnonin jahohi.
Sun kuma goyi bayan kirkiro yan sandan jihohi bisa dalilin gazawar ƴan sandan gwamnatin tarayya wajen tabbatar da tsaro.
Da yake jawabi shugaban kwamitin da gwamnatin jihar Katsina ta kafa Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida ya shaida cewa kwamitin ya riga ya sadu da kwamitin majalisar wakilai,yanzu saura Majalisar Dattijai.
“Shiyasa gwamnatin Katsina ta kafa wannan kwamiti domin bai wa ko wace shiyya uku da ke jihar su gabatar da buƙatar su,”inji Wazirin Katsina.
Taron wanda ya gudana a sakatariyar gwamnatin Jihar Katsina ya sami halartar ƙungiyoyi masu zaman kansu da alummomi daban-daban da suka fito daga yankin Daura, Funtua da Katsina,kuma dukkanninsu sun gabatar da buƙatar su ga kwamitin.
