
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin ne wata tawagar ƴan sandan da suka yi ritaya a Abuja ta karaɗe tituna inda ta yi zanga-zangar lumana game da halin rashin kula yadda ya dace da suke fuskanta da waɗanda ke aiki har yanzu a rundunar daga gwamnati.
An gudanar da zanga-zangar ne a ƙarƙashin jagorancin mai fafutukar ƴancin al’umma, Omoyele Sowore, wanda ya shiga sahun masu zanga-zangar da nufin janyo hankalin Gwamnatin Tarayya.
Sun koka game da rashin gamsuwa da yadda ake kula da su tsawon shekaru akan rashin biyan su kuɗaɗe fansho da kuma yin watsi da walwalar jami’an da ke aiki a yanzu.
A lokacin da ya ke magana yayin zanga-zangar, Sowore ya yi kira ga gwamnatin da ta dubi sadaukarwar da jami’an suke yi wajen bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma kariya da ta tabbatar da fifita walwalarsu.
Masu zanga-zangar sun yi gargaɗin cewa matuƙar ba a ɗauki matakin gyara akan lamuransu ba, za su cigaba da yin irin haka har sai an yi abinda suke fafutuka a kai.
A Jalingon jihar Taraba kuwa, an ga yadda jami’an da suka yi ritaya suka yi dandazo ɗauke da alluna masu rubutun da ke nuna rashin gamsuwa da yadda ake kula da su.
Daga cikin abinda suke neman a soke akwai tsarin tara kuɗaɗen fansho na ƴan sanda, wato Police Contributory Pension Scheme da kuma neman a biya su cikakken kuɗaɗensu na giratuti.
A ranar Lahadi Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya umarci baki ɗaya kwamishinonin ƴan sanda na jihohi da su samar da cikakken tsaro ga harkokin zanga-zangar.
