“Ban fi shekara biyu da fara karantun littafi ba na fara rubuta nawa”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Ana cigaba da samun marubuta da ke shigowa fagen harkar rubutun adabi da sabbin nazarce-nazarce, da fahimta iri daban-daban da suka dace da zamani. A yayin da wasu marubutan suka ta’allaƙa ga yin rubutu kawai don nishaɗi da ɗebe kewa, wasu kuwa ƙoƙari suke yi su yi rubutu don faɗakarwa da koyar da darussan rayuwa. Marubuta irin su Sakina Isma’il, ýar Kamaru mazauniyar Kano, na daga cikin irin waɗannan matasan marubutan waɗanda bayan ma rubutun labari har zaure musamman suke buɗewa don ilimantar da mata abubuwan da suka shafi zamantakewar aure da mu’amala ta yau da gobe. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya zanta da wannan matashiyar marubuciya da ta fito daga garin Garoua na ƙasar Kamaru.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.
SAKINA: Sunana Sakina Isma’il, amma duniyar rubutu an fi sanina da Sakina Ismail Kamaru, ko kuma Mom Muwadda. Ni marubuciya ce, kuma ýar kasuwa mai sana’ar sayar da turare. Ina kuma da shafi da nake faɗakarwa kan zamantakewar iyali da soyayya tsakanin samari da ýammata. Ina da aure, da ýata guda ɗaya.
Zan so ki bamu tarihin rayuwarki a taƙaice.
Ni haifaffiyar ƙasar Kamaru ce daga birnin Garoua. A can aka haife ni, har na yi karatu na na boko da na addini dukka. Sai dai ban yi nisa sosai a boko ba, iyakacin karatuna matakin sakandire. Naso na cigaba da karatu, amma hakan bai samu ba, sakamakon zuwana Nijeriya. Kuma yanzu haka ina zaune a garin Kano ne tare da iyalina.
Wacce irin rayuwa ki ka yi lokacin tasowarki da gwagwarmayar da ki ka sha, kawo yanzu?
Alhamdulillahi. Na taso cikin kyakkyawar tarbiyya da rayuwa mai ban sha’awa. Iyayena sun yi iya bakin ƙoƙarin su wajen ba mu kulawa da sa’ido kan tarbiyyarmu. Mahaifina mutum ne mai kula sosai, kan lamarin iyalinsa, don haka duk lokacin da ya dawo gida kafin ya zauna sai ya tambayi Mamanmu ina muke? Sai ya gan mu tukunna zai zauna ya ci abinci. Wannan dalilin ne ya sa muka saba da zaman gida, in mun je unguwa kuma duk inda ƙarfe huɗu zuwa biyar ta yi dole mu koma gida. Tun tasowata ina ƙarama ni ba mai yawan shiga hurumin kowa ba ce, ƙawaye ma iyakaci na da su a makarantar boko ko Islamiyya. Bayan wannan babu abinda yake haɗa ni da kowa sai ‘yan gidan mu.
Kina daga cikin matasan marubuta na onlayin, ko za ki gaya mana yadda aka yi ki ka zama marubuciya?
Lokacin da na zo Nijeriya ko zo in kashe ki ban sani ba da Hausa. Amma cikin ikon Allah ban fi wata uku da zuwa ba na fara iya Hausa, saboda tun da nake a rayuwata ina son harshen Hausa da ma shigarsu bakiɗaya. Ban taɓa tsammanin zan yi rubutun littafi ba, tun da babu shi a raina, saboda mu can Kamaru ba a rubuta littafin Hausa irin wannan, ko kuma ban san da shi ba, sai da Allah Ya kawo ni Nijeriya. Bayan na yi aure akwai wata ýar’uwata da take kai min ziyara lokaci zuwa lokaci, tana zuwa mu kwana biyu sai ta tafi to, a wajen ta ne na fara gani tana karatun littafi. Don in ta shiga ɗaki ta fara karatun littafi sai ta yi sama da awa uku ba a ji motsinta ba, in ta ji abin tausayi ta yi kuka. Idan ta fito na tambayeta lafiya, sai ta ce min karatun littafi take yi, sai na share ta na ce bata da abin yi. To, da haka watarana muna hanyar zuwa Kamaru na ce mata ta tura min nima na gwada karantawa, shi ne ta tura min. Tun daga ranar na fara karatun littafi, kuma tun ina karatawa in yi wata ɗaya zuwa biyu kafin na kammala, har na zo ina karantawa a kwana ɗaya na gama. Ban fi shekara biyu da fara karantun littafi ba na fara rubuta nawa na kaina.
Waye ya fara nuna miki yadda ya kamata ki yi rubutun labari?
Wata ýar’uwata ce ta fara nuna min, amma da farko ni kaɗai nake kwaɓa kayana. Ba zan taɓa mantawa ba, domin littafina na farko da na yi har na fara tunanin dakatarwa, saboda irin yadda ake cewa ba a fahimtar Hausata, wasu kuma su ce akwai kurakurai da yawa. Sai na ji gabaɗaya rubutun ya fita min a rai, amma kuma sai ina ji a can ƙasan zuciyata ana bani ƙwarin gwiwa cewa, me zai hana ki iyawa tunda kina da basirar ƙirƙira, ki cigaba kawai. Wannan dalilin ne ya sa na cigaba da rubutu, har na rubuta littattafai huɗu. Ba zan taɓa mantawa da wata marubuciya ana ce mata Maman Ihsan, ita ce ta bini ta WhatsApp take ce min littafina akwai gyara sosai, shin ina da ƙungiya ne? Na ce mata ina da ita, amma ƙungiyar tun da na shiga ba a taɓa mana gyaran komai ba. To, a ƙarshe dai ita ta ja ni ƙungiyar da ta kafa, ana ce mata Jajirtattu Writers Association. To, a nan ne ta koya min ƙa’idojin rubutu, da yadda zan saka alamar zancen wani, da yadda ake rubuta wasu kalmomi da sauran su. Har dai ta kai nima na fara nuna wa wasu sabbin marubuta kurakuransu muna gyarawa. Yanzu haka ma ina ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar tamu.
Shin kina karanta littattafan wasu marubutan? Kuma wanne littafin ki ke karantawa a halin yanzu?
E, a baya kamar yadda na faɗa, ina karanta littattafai sosai, amma tun da na fara rubuta nawa sai na daina karatun littafi. Dalili kuwa shi ne lokacin da nake ɗan samu na yi karatu, da shi nake amfani na rubuta nawa. Sai dai duk da haka, wani lokaci na kan karanta shafi ɗaya zuwa biyu in na ga an tura a zaurukan mu na marubuta, amma ba na iya bibiyar labarin wasu har ƙarshe yanzu. Amma a baya kafin na fara rubuta nawa, na fi jin daɗin karanta littattafan Khalisat Haidar, da na Billy Abdul.
Wacce marubuciya ko marubuci ne kallon kwaikwayonki, ko wacce salon rubutunta ya fara sa miki sha’awar rubutu?
Marubuciya Aisha Aliyu Garkuwa.
Kawo yanzu littattafan ki nawa, kawo sunayen su?
Na rubuta littattafai guda bakwai. A ciki akwai, ‘Ba Zan Zauna Da Kishiya Ba’, ‘Mijin Attajira’, ‘Mugun Uba’, ‘Duhu Da Haske’, ‘Mutum Ko Aljan?’ ‘Ni da ƙanin Mijina’, da kuma ‘Sanadin Rabuwarmu’.
Ki yi mana bitar guda uku daga ciki, da darussan da suke koyarwa ga mai karatu?
Kamar yadda na faɗa akwai littafin, ‘Ba Zan Zauna da Kishiya Ba’, wanda labari ne da yake magana a kan wata al’ada ta Fulani, wacce da zarar an haifi yarinya ake bata mijin aure. Wannan dalilin ne ya sa jarumin littafin aka ɗaura masa aure da wata ýar’uwarsa, a ranar sunanta. Sai dai a daren da aka ɗaura auren ‘yan fashi suka shiga rugar su suka yi musu ɓarna, tare da ƙona musu bukkokinsu, suka karkashe musu mutane da yawa. Sakamakon wannan mummunan abu da ya faru ne a wajen gudu don su tsiratar da rayuwarsu jarumin littafin ya rabu da iyayensa har da iyayen matar da aka ɗaura masa aure da ita dukka. Sai wani bawan Allah ne ya tsince shi ya kai shi gidansa ya yi masa magani da dukka abinda mahaifi ke yi wa ɗansa har ya girma ya aura masa ‘yar sa.
Shi kuma littafin, ‘Ni da ƙanin Mijina’, labari ne akan wani saurayi da yake da budurwarsa suke tsananin son juna har ba sa so su rabu, amma kuma bai iya ya aure ta ba. Ganin cewa yayansa bashi da aure, sai wannan saurayi ya yi duk yadda ya yi ya haɗa budurwar da ýaýan nasa, har suka yi aure. Burinsa shi ne, idan an yi auren, sai su cigaba da soyayyar da suke yi da ita a waje. Sai dai kash, ana yin auren budurwar da yayansa, sai yarinyar ta ce hakan ba za ta yiwu ba, dan kuwa ta ƙi amincewa su cigaba da ƙazamar alaƙar da suke yi a baya.
Akwai kuma sabon littafin da nake gab da fitarwa wanda na sa wa suna, ‘Sanadin Rabuwarmu’. Shi kuma labari ne akan wani da yake son auren ƙawar matarsa, da niyyar rama wulaƙancin da ƙawarta ta yi masa. Sai dai kash, ba su wani jima da aure ba ya gane tana cin amanarsa ta hanyar yin hira da abokinsa da kuma ƙaninsa, ta waya. Kuma duk tana soyaya da su bata taɓa sanin abokinsa da ƙaninsa ba ne. Dama shi ƙanin nasa a ƙasar waje yake karatu, a zauren sada zumunta suka haɗa, har soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu. A dalilin ta ne har ya yanke shawarar zuwa Nijeriya don ganinta, da niyyar daga nan zai tura magabatansa a yi maganar aure. A ranar da yayansa ya ɗauke shi da niyyar zai je ya ga amaryar yayan nasa, sun biya wani wajen cin abinci sai suka haɗu da abokinsa shi ma ya ce zai je ya ga amarya. To, a nan ne suka haɗu gaba ɗaya suka je, kuma bayan sun je gidan ya je ya faɗawa matarsa ta fito su gaisa da ƙaninsa da kuma abokinsa tana fitowa ta gansu ba a lokacin ne asirinta ya tonu.
Ta yaya ki ke samun jigon da ki ke rubutu akai, kuma wanne lokaci ne ki ka jin daɗin yin rubutu?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa da yardar mai dukkka.
