Gwamnatin Tinubu ba ta mayar da Arewa saniyar ware ba – Fadar Shugaban Ƙasa ga Kwankwaso

Spread the love

Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata zargin da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya yi kan cewa shugaba Tinubu na karkatar da ayyukan raya ƙasa ga yankin Kudu a yayin da aka yi watsi da yankin Arewa.

PREMIUM TIMES ta rawaito muku yadda kwana ɗaya bayan ganawa da Tinubu a fadar shugaban ƙasa a Abuja, Kwankwaso ya zargi shugaban da mai hankali wajen bunƙasa yankin Kudancin ƙasar.

Ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NNPP a shekarar 2023 ya yi wancan zargin ne a lokacin taron nazarin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya wanda gwamnatin Kano ta shirya.

“Bari na bai wa gwamnatin tarayya shawara kan rabon arziƙin ƙasa,” a cewar tsohon gwamnan Kano a ranar Alhamis.

“Bayanan da muke da su na nuna kamar dukkan kasafin kuɗin Najeriya ana hankaɗa shi ne zuwa ɓangare ɗaya na ƙasar nan.”

“Bari na ba wa masu ƙoƙarin wawushe komai shawara da su tuna cewa mafi yawan abubuwan da ake fama da su a wannan ɓangare na ƙasar nan (Arewa) a yau na da alaƙa da ƙarancin abin da ake turawa yankin.”

“Wannan ne dalilin da ya sa muke fama da matsalar tsaro, kuma muke da talauci. Wannan abu ne da ke faruwa sosai a nan kamar wutar daji,” in ji Kwankwaso.

Ya ce, mafi yawan hanyoyin da ake da su a Arewa sun lalace a yayin da gwamnatin APC ke cigaba da narƙa kuɗi a yankin Kudancin Najeriya.

“A jiya a yayin da nake dawowa Kano ta jirgi, amma sai aka yi rashin sa’a aka ɗage tashinmu da misalin ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare. Hakan ne ya tilasta min biyo hanya ta mota. Sai dai titin Abuja-Kaduna-Kano ya yi mutuƙar lalacewa. Wannan titi ne da aka fara shi tun farkon mulkin jam’iyyar APC.”

“Yanzu kuma ana ce mana akwai wani titi daga Kudu zuwa gabashin ƙasar nan – muna goyon bayan samar da ayyukan more rayuwa da duk wani abu mai kyau ga talakawa – a lokacin da gwamnati ke karkatar da kuɗin ƙasar nan da kashe su a wani ɓangare na ƙasar nan a yayin da aka yi watsi da sauran sassan ƙasar nan. Ba na ganin wannan abu ne da ya dace gwamnati ta aikaita,” a cewar Kwankwaso.

Ba ka fahimci abun ba ne – fadar shugaban ƙasa.

Sai dai mai ba wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan yaɗa labarai, Sunday Dare, ya yi watsi da zargin yana mai cewa ɗan siyasar bai da masaniya sosai game da irin ayyukan cigaba da gwamnati ke yi.

Dare ya jero wasu ayyukan cigaban ƙasa da wasu shirye-shirye da ya ce shugaba Tinubu ya yi ko ake kan yi a yankin Arewa a cikin shekaru biyu sun haɗa da:

-Titin Abuja-Kaduna-Kano
– Titin Sokoto-Badagry
-Titin Sokoto-Zamfara-Katsina

ƁANGEREN NOMA:

Kashe Dala miliyan 158.15 wajen shirye-shiryen bunƙasa noma (VCN) ga jihohi 9 a Arewa
Aikin raya ƙasa na Kolmani (Bauchi da Gombe)

  1. Shirin yaƙi da sauyin yanayi da inganta ƙasar noma (ACReSAL) — shiri ne na shekaru 6 wanda bankin duniya ke ɗaukar nauyi domin farfaɗo da filayen noma masu girman kadada miliyan 1 da magance matsalar sauyin yanayi.
  2. Shirin bunƙasa noman rani a jihar Kano wanda aka ƙaddamar a shekarar 2023 wanda gwamnatin Tinubu ke cigaba da yi.

FANNIN LAFIYA:

Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna (Arewa maso yamma)

  1. Asibitin koyarwa na Jami’ar Katsina (Arewa maso yamma)
  2. Asibitin koyarwa na Jami’ar Jos, Fulato (Arewa ta tsakiya)
  3. Asibitin Reference Hospital, Kaduna (Arewa maso yamma)
  4. Asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (Arewa maso yamma)
  5. Asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi (Arewa maso yamma)
  6. Asibitin Harmony Advanced Diagnostic Centre, Ilorin, Kwara (Arewa ta tsakiya)
  7. Asibitin gwamnatin tarayya, Nguru a jihar Yobe (Arewa maso gabas)
  8. Asibitin koyarwa na Jami’ar Jos, Fulato (Arewa ta tsakiya) — aikin faɗaɗa asibitin.
  9. Farfaɗo da asibitoci a matakin farko guda 1,000 a yankin Arewa maso yamma.

TITIN DA MANYAN HANYOYI:

  1. Titin Kano–Kongolam (Kano–Kanwar–Danja–Hadejia)
  2. Titin Yakasai–Zalli
  3. Titin mai nisan kilomita 1,068 Sokoto-Badagry
  4. Titin mai nisan kilomita 18. 258 a Gulumbe, Kebbi.
  5. Titin Abuja–Kaduna–Zaria–Kano
  6. Titin Biu–Kangiwa–Kamba–Gaya–Neja
  7. Titin Malando–Garin Baka–Ngaski–Wara
  8. Titin Koko–Besse–Zaria–Kala
  9. Titin Abuja–Kaduna–Kano (375 km)
  10. Gyaran gadar Gamboru (titin Gamboru–Ngala–Kala–Balde a Borno)
    25.Aikin faɗaɗa titin Mararaba–Keffi (43.65 km)
  11. Gina titin Lafiya (jihar Nasarawa)
  12. Titi mai hannu biyu daga Kano–Maiduguri
    28.Titi mai hannu ɗaya daga Adamawa–Taraba
  13. Titi mai hannu ɗaya Adamawa–Borno
  14. Titin Kaduna–Jos (Titi mai hannu ɗaya)
  15. Titin Zaria–Funtua–Gusau–Sokoto (Titi mai hannu biyu)
    32.Titin Zaria–Hunkuyi–Daya — aiki ne na gyaran titi a Kaduna da Kano
  16. Gina titin Dikwa–Gamboru–Ngala (49.55 km)

ƁANGAREN MAKAMASHI DA ISKAR GAS:

  1. Shimfiɗa bututun iskar gas daga Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK) (614 km)
  2. shimfiɗa bututun iskar gas a tashar Gwagwalada (a Abuja, da za ta haɗu da bututun AKK)
  3. Tashar samar da wutar iskar gas ABIBA, Kaduna (50 MW) — wanda ake sa ran zai bunƙasa wutar lantarki a jihar Kaduna.

SHIMFIDA LAYIN DOGO:

  1. Kaduna–Kano (203 km, wani ɓangare na aikin layin dogo na Legas zuwa Kano)
  2. Kano–Maradi (285 km, da zai haɗa Kano, Jigawa, Katsina zuwa Maradi da ke ƙasar Nijar)
  3. Aikin layin dogo na jihar Kaduna — da za a kashe Naira biliyan 100.
  4. Layin dogo da ke Abuja (Abuja Light Rail)

AIKIN BUNƘASA RUWA DA KASUWANCI:

samar da ayyukan raya kasa na domin haɗa Kalaba ta jihar Nasarawa da Abuja zuwa jihohin Arewa.

MANYAN SHIRYE-SHIRYE NA ƘASA:

Samar da cibiyar yaƙi da sauyin yanayi (NAGGW) — da nufin magance kwararar hamada a yankin Arewa.
43.Hukumar yaƙi da zaizayar ƙasa da hanyoyin gudanar ruwa (NEWMAP) — A yankin Arewa.

By Babaji