
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Darakta-Janar na tashar yaɗa labarai ta ‘Voice of Nigeria’ (VON), Jibrin Ndace ya ce an fara shirye-shiryen ƙaddamar da yaɗa labarai ta harshen Mandarin na ƙasar Chana a tashar.
Ya bayyana haka ne a yayin da ya jagoranci tawagarsa gudanarwa ta VON zuwa ziyara ta musamman ga Jakadan Chana ga Nijeriya, Yu Dunhai a Abuja.
Daraktan ya ce, ƙara yaren Mandarin cikin jaddawalin yarukan da ake amfani da su a tashar zai sa su kai guda tara.
Ya ce, a ancient ana amfani da yaruka takwas ne a tashar wajen yaɗa labarai, waɗanda suka haɗa da Hausa, Igbo, Yaroba, Fullanci, Turanci, Larabci da Swahili.
Ndace ya kuma ce, hakan wani ɓangare ne na shirin Shugaba Bola Tinubu na inganta ayyukan da suka shafi yaɗa labarai a Nijeriya.
Da ya ke jawabi, Dunhai ya bayyana cewa ci-gaban zai taimaka wajen zurfafa aiwatar da haɗin-gwiwa kan gidajen jaridu a tsakanin ƙasashen biyu, kamar yadda ya ke a yarjejeniyar da aka ƙulla a lokacin da Tinubu ya ziyarci Chana.
