Neja: Mutane da dama sun rasu bayan kifewar kwale-kwale a Shiroro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fasinjoji da dama sun rasu a yayin da wata kwale-kwale ta kife a Kogin Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Lamarin ya auku ne a ranar Asabar, kamar yadda Hukumar bada Agajin Gaggawa ta jihar, NSEMA ta bayyana.

A sanarwar ta fitar ranar Lahadi ta hannun Daraktan yaɗa labaranta da ayyuka na musamman, Ibrahim Hussaini, NSEMA ta ce kwale-kwalen ya nutse ne a tsakiyar kogin bayan ɗebo fasinjojin da ba a ƙayyade adadinsu ba da kayayyaki waɗanda suka taho daga kasuwar Zumba.

Daraktan ya ce, an yi nasarar ceto matuƙin kwale-kwalen tare da wasu kaɗan daga cikin fasinjojin, inda ɗayansu ke karɓar magani a Babban Asibitin garin Kuta.

Ya kuma ce, zuwa lokacin fitar da sanarwar, ba a san adadin waɗanda iftila’in ya rutsa da su ba, yayin da ake cigaba da ƙoƙarin ceto su.

Al’amarin kifewar kwale-kwale ya zama ruwan dare a Nijeriya inda a watan Nuwamban 2024 an samu irin haka a kogin Neja dake tsakiyar Nijeriya, lamarin da ya shafi fasinjoji kusan 200 da suka taho daga wata kasuwa a Jihar Kogi.

By Babaji