Korar SDP: Da ma can ba ka da alƙibla – Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki El-Rufa’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi tsokaci akan korar da Jam’iyyar SDP ta yi wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ba shi alƙibla a siyasa.

Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya faɗi hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafin sada zumunta kan dakatarwar tsawon shekaru 30 da aka yi wa tsohon gwamnan daga SDP.

Sakataren yaɗa labaran SDP na ƙasa, Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar da sanarwar a ranar Litinin, inda ya ce SDP ta ɗauki matakin ne a ƙarƙashin dokoki da tsare-tsaren jam’iyyar da kuma sashin dokar zaɓe ta ƙasa da ya ba ta damar zaɓar wanda ta ke so ya zama mambanta.

Jam’iyyar ta kuma gargaɗi mambobinta a faɗin Nijeriya kada su ƙulla wata alaƙar siyasa da shi tunda a yanzu shi ba mamba ba ne koma bai wakiltar ta a kowane mataki.

Haka kuma, jamiyyar ta nemi Hukumar Zabe (INEC) da hukumomin da lamarin ya shafa su shaida cewa El-Rufa’i daga yanzu ba ɗanta ba ne har sai ranar 28 ga Yulin 2055.

Haka ya biyo bayan da kwamitin ayyukan jam’iyyar ya sanar da cewa El-Rufa’i bai yi rajistar zama mamba acikinta ba saidai yana ikirarin shi ɗan SDP ne wajen shiga a dama da shi a harkokinta.

Lamarin da ya sauya alƙiblarsa a siyasa tun bayan da ya bayyana ficewarsa a jam’iyyar APC da sanar da komawarsa SDP.

By Babaji