Kogi: ‘Yan sanda sun gano gawar ɗan jaridar ɗaukar hoto da aka kashe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kogi ta samo gawar Ayo Aiyepeku, wanda ɗan jarida ne a ɓangaren ɗaukar hoto bayan halaka shi da wani abokin aikinsa mai suna Oulwapelumi ya yi.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa Kakakin ƴan sandan jihar Kogi, Williams Ovye-Aya ya tabbatar da faruwar al’amarin a Lokoja, Babban Birnin jihar, ranar Litinin.

Ya ce, an gano gawar mamacin ne a yammacin ranar Lahadi a wani yanki da ke kusa da ofishin WAEC da ke Crusher Zone 8 a Lokoja.

Daga nan ne aka garzaya da ita zuwa Babban Asibitin ‘Specialist’ a birnin, inda aka fara gudanar da bincike a kai domin gano haƙiƙanin abinda ya faru.

Ya kuma roƙi iyalan marigayin, abokan aiki da ɗaukacin al’umma da su samar musu duk wani bayani da zai taimaka wa binciken nasu.

By Babaji