Sojojin sama sun yi wa mayaƙan ISWAP luguden wuta a Tafkin Chadi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar sojojin sama (NAF) ta yi gagarumar nasara akan ISWAP a yankin Tafkin Chadi bayan wani mummunan hari da ta kai wa mayaƙanta inda ta halaka manyan kwamandodi a wani atisaye ta sama da ta ƙaddamar ranar Lahadi.

Kakakin rundunar, Air Komodo Ehim Ejodame ya bayyana haka a wata takarda.

Ya ce, an gudanar da farmakin ne a ƙarƙashin atisayen HAƊIN KAI, a maɓoyar mayaƙan dake yankin Arina Woje a Jihar Borno.

Wajen ya shahara da bai wa jagororin ƴan tada ƙayar-baya mafaka, inda sojojin suka yi wa shirinsu babban giɓi.

Farmakin ya biyo bayan samun wani rahoton sirri da jami’an suka yi aiki a kai, lamarin da ya taimaka wajen samun nasarar.

A baya an fafata tsakanin sojojin da mayaƙan inda aka lalata da dama daga cikin kayayyakin aikin ISWAP da mafakarsu.

Hakan ya nuna yadda rundunar ta ke aiki tuƙuru wajen daƙile ayyukan ta’addanci da ƙoƙarin tabbatar da tsaro ga ƴan Nijeriya.

By Babaji