Ƙungiyar Mata Marubuta ta shirya taron bita kan rubutun diramar radiyo

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A ci gaba da ƙoƙarin tafiya da zamani cikin harkar rubutun labari, ƙungiyar Mata Marubuta ta Women of Words ta gudanar da taron bita na wuni biyu domin koyar da mambobin ƙungiyar dabarun rubutun labarin wasan kwaikwayo na rediyo.

Taron dai an gudanar da shi ne a ɗakin karatu na Murtala Muhammad da ke kan titin Ahmadu Bello a cikin garin Kano, inda ya samu halartar ‘yan ƙungiyar daga ciki da wajen Kano.

Da take yi mana bayani a kan manufar shirya taron. Marubuciya Sanah S Matazu ta bayyana mana manufar taron bitar da cewa, “To yadda taron dai ya samo asali ƙungiyar Mata Marubuta ita ce ta ba mambobin ta aikin koyo, a cikin mambobin guda talatin da wani abu aka samu mutane sama da goma suka yi. Don haka ne ƙungiyar ta ɗauke su a matsayin waɗanda za a horas. Don haka sai ƙungiyar ta ɗauki nauyin malamin da zai koyar, abinci, wajen da za a yi taron da katin shaida da za a raba, wanda a farko iya mambobin ƙungiyar za a yi wa, amma daga baya aka bayar da dama ga wanda ba ɗan ƙungiyar ba za ta iya yin rajista wanda da kuma a haka aka gudanar da taron wanda Al-Mustapha Adam Muhammad ya koyar da mu na tsawon wuni biyu.”

Ta ƙara da cewa ” Kuma gaskiya an wayar mana da kai a kan rubutun radiyo dirama. Ka san marubuci bai kamata a ce ya tsaya a waje guda ba. Dole sai yana faɗaɗa ilimin sa , kuma ka ga kamar rubutun radiyo dirama ɗin duk da ba wai babu yawaitar sa ba , amma dai ya fi rubutun fim tsada, kuma ya fi shi wahala, don ba kowa yake yin sa ba, musamman marubuta mata ba su da yawa da suke rubutun radiyo firama, sai a yanzu da aka samu irin mu da muke cikin marubutan onlayin, sai dai kuma yawancin su ba su da sani a kai, amma ana amfani da su, su rubuta su bayar a yi amfani da rubutun, amma ba lallai ne diramar ta fita da sunan su ba.

To shi ya sa muka shirya wannan taron aka yi wa ‘yan ƙungiyar mu karin haske. Kuma Alhamdulillah, tun da bayan an yi bitar har an gwada an gani, kuma da yawa sun fuskanta, kawai sai dai mu ce a daure a ci gaba da samun ƙwarewa a kan abin da aka koyar da mu.”

By ukarofi