Shugabannin jam’iyyu 23 a Kaduna sun sauya sheƙa zuwa PDP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna ta samu gagarumar kamu, yayin da shugabannin jam’iyyu guda ashirin da uku (23) daga ƙananan hukumomin Maƙarfi da Kudan suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar tare da dubban magoya bayansu.

Sabbin ‘yan jam’iyyar sun fito daga jam’iyyun adawa APC, NNPP, LP da wasu ƙananan jam’iyyu. Taron sauya sheƙar ya gudana a wani gagarumin gangami da aka shirya a Maƙarfi, ƙarƙashin jagorancin Hon. Umar Shehu Ajilo, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Maƙarfi/Kudan a Majalisar Tarayya.

A wajen taron, Hon Ajilo ya bayyana cewa sauya shekar ya nuna karara yadda jama’a ke ƙara gamsuwa da manufofin jam’iyyar PDP da kuma rashin jin daɗin salon mulkin da ke tafiya a yanzu daga bangaren gwamnatin jihar da tarayya. 

“Wannan babban abu ne da ke tabbatar da cewa PDP na dawo da martabarta da amincewar jama’a,” inji shi.

Shugaban matasan PDP na ƙasa, Muhd Kadade Suleiman, wanda ya halarci taron, ya yabawa shugabannin da suka sauya sheka bisa jarumtar su na dawo da martaba da adalci a siyasa.

Ya kuma jaddada cewa PDP za ta ci gaba da karɓar kowa hannu bibbiyu domin gina Nijeriya da Kaduna mai inganci.

A jawabinsa, Isa Mohammed Ashiru, ya bayyana cewa wannan sauya shekar wata alama ce ta sake fasalin siyasar jihar Kaduna. 

“Lokaci ya yi da mu gyara gida, mu dawo da martabar jiharmu ta hanyar komawa jam’iyyar da ta gina jihar nan da ƙasa gabaɗaya – wato PDP,” inji shi.

By ukarofi