Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce ɗan wasan tsakiyar ƙungiyar, Rodri ya sake jin rauni kuma da wuya ya murmure kafin hutun watan Satumba.
ɗan ƙwallon na Sifaniya ya shafe mafi yawan kakar bara a gadon jinya saboda turguɗe gwiwa da ya yi a watan Satumban 2024.
Mai riƙe da kambin Ballon d’Or na 2024, ya koma taka leda a matsayin canji a wasan ƙarshe na Man City na gasar Premier League da ta buga da Bournemouth.
Sai kuma wasan da Al-Hilal ta fitar da su daga gasar Club World Cup a Amurka, inda aka yi canjinsa daga baya.
“Rodri na samun sauƙi saboda ya ji babban rauni a wasan da muka kara da Al-Hilal,” inji Guardiola.
