
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Jibiya/Kaita a Majalisar Wakilai, Sada Soli ya koka game da harin ƴan bindiga akan masallata a Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
Iftila’in ya auku ne kwanaki uku da suka gabata a wani masallaci yayin sallar asuba, inda ya ce baya ga jami’an tsaro sun san su, kuma suna riƙe da iko a wasu yankunan jihar.
A wata hira da shi ta gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, ɗan majalisar ya ce ƴan bindigar da suka kai harin, suna gudanar da harkokinsu cikin walwala a ƙauyukan da ke iyaka da jihar Zamfara.
“Su ne waɗanda suke da iko a jihar. An san su, musamman a yankunan Ƙanƙara da ke iyaka da jihar Zamfara.”
Ya ƙara da cewa, “sun shiga Ƙanƙara, sannan suka shiga Malumfashi, sannan suka shiga Funtua a wannan ɓangaren. Akwai ƙananan hukumomin da suka raba iyaka. Waɗanda su ne ƙalubalen.”
Ɗan majalisar ya kuma yi watsi da batun da ke cewa maharan wasu ne daga waje, yana mai cewa mutane ne da ke cikin ƙauyuka.
Bugu da ƙari, ya ce ba za a iya magance matsalar rashin tsaro a mataki na jihar ba kaɗai, saidai abu ne da ke buƙatar agajin gwamnatin tarayya don kauce wa faruwar irin haka a nan gaba.
A ranar Laraba gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasuwar masallata guda 32 yayin aukuwar harin, wanda ya faru a garin Mantau, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.
