Shari’a ta zama abin sayarwa yanzu a Nijeriya – Sarkin Musulumi ga NBA

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sarkin Musulumi, Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku ya yi gargaɗin cewa shari’a a Nijeriya ta ɗauko hanyar rasa martabarta duba da yadda ta ke fifita masu kuɗi akan talakawa a yayin hukunci.

Sarkin ya faɗi haka ne yayin gabatar da jawabi a babban taron Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta 2025 da ake yi a Enugu, ranar Lahadi, wanda masana harkar shari’a da alƙalai da dama suka samu halarta.

A cewarsa, rashawa da rashin daidaito sun yi katutu a harkokin shari’a a Nijeriya ta yadda al’umma suke ƙaurace wa cigaba da yarda da samun adalci a yayin shari’a.

Ya ce, a yau rashin adalci ya zama abin saye da kuɗi inda galibin waɗanda ke faɗa wa tarkon hakan sune talakawa yayin da masu kuɗi ke aikata manyan laifuka kuma suke cigaba da zirga-zirga cikin walwala a gari.

Ya kirayi mambobin ƙungiyar da su kauce wa dukkan ayyukan da suka saɓa wa doka ko waɗanda za su yi sanadin rage darajarsu a idon al’umma, yana mai cewa adalci na gaskiya ba ga masu kuɗi kaɗai aka samar da shi ba.

Ya kuma yi gargaɗin cewa dukkan tsarin shari’ar da ya gaza tsayar da gaskiya da adalci ka iya rugujewa, yana mai kira ga lauyoyi da su yi amfani da taron wajen tattauna yadda za a shawo kan matsalolin da suka dabaibaye Nijeriya.

By Babaji