Daga MUKHTAR YAKUBU
An yi kira ga iyaye su sanya idanu game da irin finafinan da yaran su suke kallo domin kaucewa haɗarin da hakan yake haifarwa musamman a wannan lokaci na Soshiyal Midiya.
Sarkin ya yi wannan Kiran ne a ranar laraba 20 ga Agusta 2025 lokacin da shugaban hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano Abba El-Mustapha ya kai mai ziyarar girmamawa tare da goyon bayan masarautar Kano bisa yaƙin da suke yi na kawar da abubuwan da suke lalata rayuwar matasa a wannan lokacin.
Sarkin ya ce ‘ wannan ayyukan da hukumar tace finafinai take yi abubuwa ne masu kyau da ya kamata a yaba mata, domin kuwa a cewar sarkin, mu a wannan Ƙasar ba mu da tsari na bin dokar kallon finafinai wannan ya sa ba a bambance fim ɗin da yara za su kalla da kuma wanda manya za su kalla, don haka abu mafi muhimmanci shi ne iyaye su kula da me yaran su suke kallo musamman a waya idan dare ya yi. Saboda yaran mu matasa a yanzu suna ɓata lokaci cikin dare suna kalle-kallen abubuwan da ba su dace ba a tashoshin da ake nuna finafinai na batsa. Don haka iyaye su rinƙa sanya ido.
Tun da farko a nasa jawabin, na maƙasudin zuwan nasu fadar Sarkin Kano, shugaban hukumar tace finafinai Abba El-Mustapha. Ya ce
” Mun zo wannan fada ne ta Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ll domin gaisuwar girmamawa da kuma neman goyon bayan masarautar domin gudanar da ayyukan da za su kawo gyara da kuma kyautatuwar tarbiyyar matasa da ɗora su a kan hanyar da ta dace da addini da kuma al’adu na Jihar Kano.
Wannan tun daga lokacin da mai girma Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ɗora mana wannan nauyi muke ta ƙoƙari wajen sauke shi ta hanyar haɗa kai da sauran hukumoni malamai da uyayen mu sarakuna. Don haka mun jaddada neman goyon bayan masarautar Kano da kuma neman ta umarci hakimai da dagatai wajen samun goyon bayan su a bisa wannan aiki namu. Domin muna son nan gaba kaɗan za mu yi rangadin ƙananan hukumomi 44 da muke da su a wannan jihar don gudanar da ayyukan”.
Ya ƙara da cewa” Daga cikin irin muhimman ayyukan da muka gudanar akwai gyara a harkar yadda ake gudanar da fim da horas da kurame yadda za su yi fim domin su samu damar cin moriyar fasahar da suke da ita a kan harkar.
Haka nan mun shirya taron Mauludi da ƙungiyoyi Sha’irai na Jihar Kano domin haɗa kan su da kuma nuna musu yadda za su gudanar da ayyukan su cikin girmama lafazi da kuma kalaman da za a yi yabon Manzon Allah da shi.
Haka nan mun samar da tsari na yadda za a yi tallan magugunan gargajiya da lasifika, saboda yawan ƙorafi da ake yi na kalaman batsa da suke yi a cikin tallan nasu.
Sannan su ma marubutan littattafai mun shirya musu gasa domin a jawo su jiki a nuna musu muhimmancin su a cikin al’umma.
Da akwai dai abubuwa masu tarin yawa da muka gudanar na kawo gyara a wannan jiha tamu mai albarka, don haka muke ƙara neman goyon bayan Masarautar Kano domin ci gaba da faɗaɗa ayyukan mu.”
Abba El-Mustapha dai ya samu rakiyar wasu daga cikin manyan ma’aikatar sa da suka haɗa da daraktan kula da tsara fim. Daraktan ɓangaren ɗab’i da akawun hukumar da sauran ma’aikatan hukumar.
