
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da sabon gargaɗi ga jihohin arewa guda tara sakamakon yiwuwar samun mamakon ruwan sama a tsakanin ranakun 25 da 29 ga watan Agusta, 2025, lamarin da ka iya haddasa ambaliya a garuruwa da dama.
Daraktan Reshen kula da lamuran ambaliya da yankuna masu barazanar ambaliya a Ma’aikatar Muhalli, Usman Abdullahi Bokani ya bayyana haka a wata takarda, ranar Litinin a Abuja.
A cewar sanarwar, Cibiyar Gargaɗin Ambaliya Akan lokaci (FEW Centre) ta bayyana sassan wasu jihohi a matsayin wuraren da ka iya fuskantar gagarumar ambaliya.
Jihohin sune; Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Sakkwato da Zamfara.
Bokani ya kuma ce, garuruwan suna halin fuskantar mamakon ruwan sama a ƴan kwanakin nan, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakan kariya domin kauce wa iftila’in.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihohin da lamarin ya shafa da su kasance a ankare, sannan su riƙa aiko da rahoto akai-akai ta yadda za a shawo kan matsalar yayin da ta ke ƙoƙarin tunkarar yankunan.
Ga wasu daga cikin sassan a jihohi kamar haka:
Adamawa: Mubi, Shelleng, Abba-Kumbo
Katsina: Katsina, Kaita, Bindawa
Jigawa: Gwaram
Gombe: Nafaɗa
Borno: Ngala
Kano: Sumaila
Zamfara: Anka
Sakkwato: Makira
Bauchi: Azare da Jama’are.
