
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a samar da ƙungiya ta dindindin ga jagororin tsaro na Afirka a matsayin ɓangare na ƙarfafa haɗakar tsaro tsakanin ƙasashen nahiyar.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin buɗe babban taron shugabannin tsaro na Afirka a Abuja, wanda aka gudanar a ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025.
Shugaban Ƙasar, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilce shi, ya ce daga yanzu Afirka ba za ta cigaba da amfani da salo marasa ƙarfi ba wajen daƙile ayyukan ta’addanci, waɗanda suka haɗa da garkuwa da mutane daga ƴan bindiga, sata a yankunan ruwa da yanar gizo da kuma rikicin siyasa.
Ya ce, kafa irin ƙungiyar zai taimaka wajen tabbatar da cigaba da tattaunawa tsakanin jagororin don samun wata maslaha da ta shafi tsaro, zurfafa yarda tsakanin dakarun sojoji da kuma bada tabbacin magana akan tsaro da murya ɗaya a Afirka.
Kazalika, ya bayyana cewa samar da tsaro mai ɗorewa ginshiƙi ne ga cigaban nahiyar, inda ba a iya samun gagarumin ci-gaba a hali na rashin tsaro.
Haka kuma, Tinubu ya kirayi ƙasashen Afirka da su inganta lamuran hukumomin tsaro da kare kayayyakin fasaharsu daga kulawa daga ƙasashen waje, lamarin da ka iya haifar wa ƙarfin shugabancin ƙasa koma-baya.
