Ta’addanci: An sace mutum 4,722, an biya fansar biliyan N2.57 a shekara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matsalar tsaro a Nijeriya ta haifar da abin da masu sharhi a yanzu ke kwatantawa da “illar tattalin arzikin biyan kuɗin fansa,” inda ayyukan satar mutane fda yin garkuwa da su, don neman kuɗin fansa suka zama tamkar wata sana’a.

Hukumar Binciken Siyasa da Tsaro (SBM) ce ta fitar da rahoto kan yawan biliyoyin Naira da ‘yan bindiga ke karɓa a hannun mutane da sunan kuɗin fansa.

Rahoton ya bayyana cewa, masu garkuwa da mutane sun buƙaci sama da Naira Biliyan 48 daga hannun jama’a tsakanin Yuli 2024 zuwa Yuni 2025.

Hakan ya na cikin sabon rahotonsu da suka kira “Economics of Nigeria’s Kidnap Industry”.

Rahoton ya bayyana cewa daga cikin wannan adadi na biliyoyi da aka nema, an biya biliyan N2.57 ne kacal ba ƙari.

SBM ta ce aƙalla mutane 4,722 aka sace a hare-hare 997, inda mutane 762 suka mutu a wannan lokaci.

SBM ta bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma ne mafi muni, yayin da Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu ke fuskantar satar saboda addini da neman kuɗi.

Misali, a rahoton 2022 an biya miliyan N653.7 wanda ya yi daidai da Dala miliyan 1.13, sai ya sauka zuwa miliyan N302 a 2023.

Rahoton ya ce wannan bambancin ya nuna yadda ake samun koma-baya a darajar Naira, wanda ya ƙara sa garkuwa da mutane zama babbar sana’a.

SBM ta bayyana cewa masu laifin suna ƙara buƙatar Naira mai yawa domin su daidaita da raguwar ƙarfin sayen kuɗin ƙasar.

Rahoton ya ƙara da cewa, hakan ya sauya garkuwa daga matsalar tsaro kawai zuwa wata sana’a da ke ci gaba da bunƙasa.

A nazarin jihohi, an gano cewa Zamfara, Kaduna da jihar Katsina sun fi yawan waɗanda aka yi garkuwa da su a cikin wannan shekara.

“A lokutan da aka yi wannan bincike, Katsina ce kan gaba da yawan kai hari har sau 131 da ya kai kashi 13 a Nijeriya baki ɗaya.

“Sai dai hakan ya gaza da yawan mutane da aka sace a Zamfara ba wanda ya kai jama’a 1203, hakan ya kai kashi 24 kenan.”

SBM ta ce daga cikin jihohi biyar da ke gaba a yawan hare-hare, huɗu daga Arewa ne, ciki har da Katsina, Kaduna, Zamfara da Neja.

Delta ce kaɗai daga Kudu ke cikin jerin, inda aka samu hare-hare 49, wanda bai kai kashi 5 na gaba ɗaya ba.

By ukarofi