Neja: Fusatattu sun ƙone mai sanannen shagon abinci da rai kan ɓatanci ga Annabi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu fusatattu sun ƙone wata mata mai shahararren shagon sayer da abinci da ranta a garin Kasuwan-Garba da ke Ƙaramar Hukumar Mariga a jihar Neja, bayan zargin ta da ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, matar, wadda aka sani da suna Amaye, ta furta kalaman ɓatancin ne a lokacin da take tattaunawa da wani kwastoma a shagon abincin nata.

Wani shaida ya ce, al’amarin ya faro ne a lokacin da kwastoman cikin wasa ya yi mata tayin aure inda ya ba ta misali da sunnar manzon Allah (SAW), lamarin da ya sa ta bada amsa cikin fushi da furta munanan kalamai akan addinin musulunci.

Jin haka ke da wuya, mazauna yankin suka ɗauke ta zuwa wajen Hakimin Kasuwan-Garba.

Daga nan ne hakimin ya miƙa ta ga jami’an tsaro domin su yi bincike akanta.

Ana tsaka da haka ne fusatattun al’ummar da ke wajen suka banƙara jami’an tsaron tare da fizgo matar, inda suka banka mata wuta.

Rundunar ƴan sandan Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda daga Kakakinta, DSP Wasiu Abiodun, ranar Asabar.

Ya ce, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na rana a ranar 30 ga Agusta, 2025.

Ya kuma ce, tuni aka baza jami’an tsaro a yankin domin kwantar da tarzoma, yana mai cewa rundunar ba za ta amince da ɗaukar doka a hannu ba acikin al’umma.

By Babaji