Daga AISHA ASAS
Rahotanni daga kafofin watsa labarai sun nuna cewa an fara tattaunawa da manyan jarumai biyu Amitabh Bachchan da Shah Rukh Khan, domin su fito a cikin sabon fim ɗin Don 3. Wannan fim za a shirya shi ne tare da sabon tauraron zamani Ranɓeer Singh.
Idan wannan labari ya tabbata, zai kasance karo na farko da manyan jarumai uku daga ƙarni daban-daban suka haɗu a fim ɗaya. Wannan na nufin haɗuwar tarihin Bollywood tun daga shekarun 1970s (lokacin Amitabh), zuwa shekarun 1990s da 2000s (lokacin Shah Rukh), sannan zuwa zamanin yanzu (Ranɓeer).
Masu fashin baƙi a harkar fim sun bayyana wannan a matsayin wani babi mai tarihi. Magoya baya kuma sun cika shafukan sada zumunta da kalaman murna da fatan ganin wannan haɗin gwiwa a zahiri.
