Tsadar ciwon ƙoda

Spread the love

Tare da CHIROMA AMINU ASID

Wannan rashin lafiyar zai shanye Naira miliyan 50 zuwa 60 a cikin aljihunka. Ciwon ƙoda mummunan ciwo ne, yana daga cikin cuta mai hatsarin gaske da ake kamuwa da ita acikin al’umma. Saboda haka, ku bayar da hankalinku da lokacinku wurin karanta wannan rubutun mai amfani.

ƙoda ita ake kira “Kidney” da Turanci. Kowa ne mutum yana da ƙoda guda biyu a cikin cikinsa.

Mene ne amfanin wannan ƙodar?

ƙoda tana amfani domin tace jini. ƙoda kamar tsintsiya ce da ke share dukkan dattin da ke a cikin jinin ɗan adam.

A kowacce rana, ƙoda tana tace jinin mutum sau 30 zuwa 40. Babu wani mashin ko na’ura da za ta iya wannan aikin a sauƙaƙe. Tsarki ya tabbata ga Allah subuhanahu wata’ala.

Idan ƙodar mutum ta tsaya da aiki, jinin jikinsa zai kasance gurɓatacce marar kyau har zuwa lokacin da ya samu lafiya. Idan aka samu gurɓataccen jini a cikin jiki, sauran sassan jiki irinsu zuciya, hanta, ƙwaƙwalwa, hanji da tsokokin jiki duk matsalar za ta iya shafar su.

Wannan ya sa idan mutum yana fama da matsalar ƙoda, jikinsa zai kumbura tare da rashin kuzari da ciwon gaɓoɓin jiki.

Duk mutumin da ƙodarsa ta gaza, yana da zaɓi biyu:

1. Za a ci gaba da yi masa wankin ƙoda, abin da ake kira ‘dialysis’ da Turanci. Shi wannan dialysis, wani mashin ne da ake amfani da shi, domin wanke dattin jini zuwa wani ɗan lokaci. Kuma wannan mashin ba zai iya aikin da ƙoda ke yi ba, domin kuwa ƙoda na wanke jini sau 30 zuwa 40 kowace rana. Amma ‘dialysis’ sau uku ake yi a cikin sati.

2. Mataki na biyu shine a yi tiyatar dashen ƙoda akan kuɗi Naira miliyan 30 zuwa 40. Wannan matakin na biyu ya fi ƙarfin talaka. Bayan an yi tiyatar dashen ƙoda, akwai jinya da shan magani, wanda shi ma zai iya cin miliyoyin kuɗi. Ko a cikin garinku mutum nawa ka taɓa gani an yi wa tiyatar dashen ƙoda? Aiki ne mai matuƙar wahala da tsadar kuɗi, wanda za a iya sayar da dukkan kadarorin da iyalanku suka mallaka a duniya.

Mene ne mafita?

Wacce hanya mutum zai bi domin kare ƙodarsa daga lalacewa?

1. Ku ajiye shaye-shaye (sigari, wiwi, giya ko ƙwayoyin magani ba bisa ƙa’ida ba).

2. Ku ajiye shan jiƙe-jiƙen kayan bauri da ba su da amfani.

3. Ku rage yawan cin gishiri a cikin abincinku.

4. Idan ka san ka na da ciwon hawan jini ‘high blood pressure’ ko ciwon sikari ‘diabetes’, to dole ka mayar da hankali wurin zuwa asibiti akai-akai, domin gwaji da rubuta maganin da ya dace.

5. Yawan shan tsaftatattun ruwa akai-akai. Dole mutum ya nemi tsaftatattun ruwan sha tare da guje wa gurɓatattun ruwan sha. Ba kowane irin ruwa ake sha ba.

6. Cin lafiyayyen abinci mai gina jiki da ’ya’yan itace ko ganye. Ku guje wa cin abinci mai kitse ko maiƙo sosai.

7. Motsa jiki akai-akai (gudu, ƙwallon ƙafa, tafiya a ƙafa da sauransu).

A ƙarshe kuma, idan ka na fama da matsalolin ƙoda ko kumburin jiki, to ka je assibiti, domin ganin likita a hukumance.

By ukarofi