NSCDC da abokan hulɗa sun haɗa kai domin kariya ga muhimman kadarorin ƙasa a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Hukumar tsaro ta sibil depens (NSCDC), reshen Jihar Gombe, ta ƙaddamar da sabon mataki na kare M
muhimman kadarorin ƙasa da muhimman ayyuka (CNAI) ta hanyar gudanar da zaman farko na haɗin gwiwa tare da manyan masu ruwa da tsaki a jihar.

Taron, wanda Kwamandan Jihar, Jibrin Idris, ya jagoranta, an gudanar da shi ne bisa ga umarnin babban kwamandan NSCDC na ƙasa, Farfesa Ahmed Audi, da kuma sakamakon taron haɗin kai da aka gudanar a ofishin mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa (NSA).

A jawabin sa, Kwamanda Idris ya jaddada cewa, akwai umarnin doka da ya rataya a wuyan hukumar wajen kare muhimman wurare da cibiyoyi a faɗin ƙasa, yana mai cewa wannan aiki ba zai yiwu ba sai da haɗin gwiwa daga kowa da kowa.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Superintendent Buhari Sa’ad, ya fitar, an bayyana cewa hukumar ta riga ta gana da shugabannin hukumomin tsaro a jihar, inda suka yi alƙawarin goyon baya ga shirye-shiryen NSCDC.

Sanarwar ta ƙara da cewa tattaunawar ta maida hankali ne kan yadda za a ƙarfafa haɗin kai, inganta musayar bayanan sirri, kafa tsarin gaggawar ɗaukar mataki, da kuma tabbatar da cewa duk masu ruwa da tsaki su riƙa sanar da NSCDC cikin sa’o’i 24 idan aka samu kama da ke da alaƙa da laifukan da suka shafi CNAI.

Cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilan hukumar kula da man fetur ta tsakiya da ƙasa (NMDPRA), hukumar haraji ta ƙasa (FIRS), Kamfanin man fetur na ƙasa/Nigerian Petroleum Supply Company (NNPC/NPSC), kamfanin raba wutar lantarki na Jos (JED), Hukumar Wayar da Kan Jama’a (NOA), ƙungiyar aikin yi ga matasa (NYSC), Kamfanin MTN Nigeria, da kuma mataimakin shugaban Jami’ar North Eastern University, da sauransu.

Kwamanda Idris ya kuma bayyana shirin ƙara wayar da kan jama’a ta hanyar kafafen watsa labarai da kuma gina tsare-tsaren kariya tare da masu kula da CNAI. Ya jaddada cewa kare muhimman kadarorin ƙasa “alhakin haɗin gwiwa ne da ke buƙatar haɗin kai, tsaro a koda yaushe, da cikakken jajircewa daga duk masu ruwa da tsaki.”

By ukarofi