Daga MAHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban matasan Kwankwasiyya, kuma mataimakin shugaban matasan jam’iyyar NNPP na Jihar Ribas, Hon. Kabiru Libda ya bayyana cewa ganin yadda suka yi wa jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya hidima ta hanyoyi daban-daban har kuma ɗan takarar shugaban ƙasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya samu ƙuri’u masu yawa a Jihar Ribas a zaɓen gamagari na 2023, wanda kuma a cewarsa suka wayar da kan ‘yan uwansu na Jihar Kano da gagarumar gudunmawa, wanda hakan tasa abokan da masoyan da duk wanda zasu gaya masa ya ji Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zaɓa a zaɓen gwamna, haka duk sauran zaɓuɓɓuka da sauran muƙamai a Kano mutanen mu NNPP Kwankwasiyya suka zaɓa amma yau shekara biyu ba a waiwaye mu ba kuma ba a mana komai ba duk da gudunmawar da muka bada, don haka wannan dalili ya sa muna dab da barin Kwankwasiyya a Jihar Ribas kamar dai yadda shugaban matasan Kwankwasiyya na jihar ya faɗa.
Har ila yau ya ce da ya suna labarin waɗansu daga wajen Kano suka bada gudunmawa irin wannan kuma ƙasa da irin tamu ko sam da tamu gudunmawar gajiyar gwamnatin Kano amma mu jagororin da suke Kano sun manta da mu kafin zaɓe suna ɗaukar zaɓe suna ɗaukar wayoyin bayna zaaɓe tasanhar abokan hamayyarmu na goranta mana ai kwankwasiyya kenan baku sani ba ne kamar yadda Hon Libda ya shaidawa Biueprint Manhaja.ya ce daga cikin jagororin namu da basa ɗaukar wayar mu a yanzu Hon AB Mahmud Shugaban ƙaramar Hukuma Bunkure, Hon Hashin Dungurawa Shugaban Jamiya NNPP na Kano akwai Arct Hon DG Yusuf Zarewa shugaban hukumar ƙawatar birnin Kano sai kuma shugaban gidan namun daji na Kano MD Sadik Muhammad Kura sai kuma mai Bawa Gwamanan Kano shawara a Fuskar Siyasa Hon Sunusi Surajo Kwankwaso wanda duk sunyi watsi damu bam ai ɗaukar wayra mu dob haka muna sanar da jagoran kwankwasiyya halin da muke ciki da kuma Shirin da muka yi na barin NNPP Kwankwasiyya a Jahar Ribas Hon Libda wanda aka fisani da da Babba Ribas Fatakot Nijeriya.
Sai kuma a nasa ɓangaren mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkar siyasa Hon Sunusi Surajo Kwankwaso ya faɓa a wata hira da manema babu wani wanda ya ma Kwankwasiyya hidima bai mori Gwamnatin Abba wanda bai zaɓi gwamnatin ba ya ci gajiyarta don haka sai dai wanda ke amfani da sunan Kwankwasiyya ba ɗan Kwankwasiyya amma shi da kansa a matsayinsa na mai bawa gwamna shawara a fuskar siyasa yan Kwankwasiyya da dama sun zo nan ofshina na taimamaka musu kuma mutanan mune yan Kwankwasiyya na jihar Ribas kuma zamu cigaba da taimak musu a cewar Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso kan zargi da ƙorafi da shugaban matasan kwankwasiyya na Jahar Ribas Hon. Kabiru Libda na cewa jagororinsu na Kwankwasiyya na Kano bayan cin zaɓe Gwamnan Kano.
