Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe
Cibiyar nazari da magance matsalolin cin zarafi a gida (CERSDOV), tare da goyon bayan Gwamnatin Norway da asusun raya jama’a na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA), ta faɗaɗa yaƙin wayar da kai kan ’yancin lafiyar haihuwa (SRHR) da kuma yaƙi da cin zarafin mata (GBV) zuwa ƙananan hukumomin Akko da Billiri a Jihar Gombe.
A yayin taro da kungiyoyin mata a Kumo, babban mai bincike na CERSDOV, Dokta Hussaini Momoh Lawal, ya bayyana cewa wannan ziyartar ta ƙunshi duba tasirin shirye-shiryen da aka aiwatar a matakin al’umma, bayan jerin horo da aka gudanar tare da tallafin Norway da UNFPA.
Ya buƙaci mata da su ci gaba da karya shingayen al’ada domin tabbatar da ingantacciyar kariya ga kansu da kuma ’yan mata masu tasowa.
Itama jakadiyar CERSDOV wacce kuma lauya ce a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Gombe, Mwalin Naomi Abdu, ta jaddada cewa kawo karshen cin zarafi na bukatar hadin kan iyaye, gwamnati, shugabannin addini da na gargajiya.
A Akko, jakadun da aka horar sun bayyana cewa shirin ya ƙarfafa musu fahimtar yadda za su fuskanci matsalolin GBV da SRHR, tare da ci gaba da tattaunawa da mata da ’yan mata kan hanyoyin magance irin waɗannan matsaloli da kuma samun dogaro da kai.
Shugaban Da’awa na Akko, Mamman Alhaji Buba, wanda kuma shi ne mai kula da cibiyar kare haƙƙin yara, tare da shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Akko, Fasto Barnabas Yakubu Faruq, sun yaba da shirin, inda suka yi kira da a ƙara haɗa kai daga maza da shugabannin al’umma domin ɗorewar wannan yaƙi.
A Billiri kuwa, mata sun bayyana cewa raguwar ƙararrakin fyade da cin zarafi ya samo asali ne daga cigaba da wayar da kai da kuma faɗakarwar da CERSDOV ke gudanarwa tare da goyon bayan Gwamnatin Norway da UNFPA.
