Da Buhari ya mayar da hankali akan ɗorewar al’amuran ƙasa madadin yaƙi da rashawa – Fasto Kukah

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban jagoran al’ummar Kirista na Jihar Sakkwato Matthew Hassan Kukah ya bayyana cewa ina ma ace Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya fifita ɗorewar al’amura da haɗin kan al’umma a zamanin mulkinsa sama da yaƙi da rashawa a ƙasar da ke a rarrabe.

Ya ce, yaƙi da rashawa abu ne da ke da muhimmanci wajen ciyar da ƙasar gaba, amma haɗin kan al’umma da ɗorewar al’amura su suka fi muhimmanci.

Babban faston ya kuma ce, akwai buƙatar Gwamnatin Tarayya ta ƙara himma wajen kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya da warware matsalar ƙoƙarin ɓalle wa daga ƙasar daga ƴan yankin al’ummar iyamurai don kafa ƙasar Biafra.

Da yake ganawa da manema labarai a Kaduna yayin bikin cikar shekera 50 na Nostra Aetate, Fasto Kukah ya kirayi Shugaba Bola Tinubu da ya mayar da hankali wajen tabbatar da ɗorewar al’amura da haɗin kan al’umma a ƙasar.

Ya ƙara da cewa, idan babu zaman lafiya, aiwatar da muhimman tsare-tsaren gwamnati abu ne da ka iya samun cikas domin al’umma ba za su samu nitsuwa ba wajen biyayya a gare su.

Haka kuma ya ce, sanya su cikin harkokinsu na kullum abu ne da ka iya ba su wahala a sakamakon rashin kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankunansu.

By Babaji