Boko Haram ta yanzu na iya zama wasan yara idan ba a ɗauki mataki ba – Obasanjo

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya magantu kan ƙaruwar al’umma a Nijeriya, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a magance matsalar ba zai iya haifar da mummunar illa.

A lokacin da yake jawabi a Sakkwato a wajen ƙaddamar da Cibiyar ICT ta Bakhita a Sakatariyar Katolika, tsohon Shugaban ya jaddada muhimmancin ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban aasa.

“A shekara ta 2050, mutane irin su Sultan za su kasance a nan, ba ina addu’ar zama a nan shekaru 25 na gaba ba ne,” inji Obasanjo.

“Za mu fuskanci matsalar ‘yan Nijeriya miliyan 400 da za a samar musu da abinci da ayyukan yi. Idan muka kasa shiryawa, Boko Haram na yau za su zama wasan yara, dole ne mu kula da wannan yanayi a yanzu.”

Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi haɗin kan ƙasa a cikin mabambantan ra’ayi da kuma bijirewa labaran waje da ke ɓata aasar.

“Idan bambancin mu yana tafiya tare da kyakkyawan shugabanci tare da kowa da kowa, to za mu kai labari.”

Ya yabawa Bishop Hassan Matthew Kukah bisa jagorancin aikin ICT, Obasanjo ya bayyana shi a matsayin wani wuri ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya, ba tare da la’akari da addini, ƙabila, ko jinsi ba.

Shi ma da yake nasa jawabin, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III Sultan Abubakar ya yaba wa Obasanjo bisa wannan karramawar da aka yi masa, ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi koyi da jajircewarsa wajen inganta haɗin kai.

Ya kuma jaddada buƙatar ‘yan Nijeriya su haɗa kai wajen magance matsalolin tsaro da kuma samar da ci gaba.

Alhaji Aminu Dikko, wanda ya wakilci Aliyu, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Sokoto, ya nuna jin daɗinsa ga Obasanjo da cocin Katolika bisa wannan shiri.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da jajircewa wajen bunƙasa ilimin fasaha domin faɗaɗa damammaki ga al’umma masu zuwa.

By ukarofi