Kocin Nottingham Forest, Ange Postecoglou ya buƙaci magoya baya su kara haƙuri, bayan da har yanzu bai ci wasa ba.
Ranar Alhamis Forest za ta karɓi baƙuncin Midtjylland a Europa League a City Ground a karon farko tun bayan kusan shekara 30 rabon da ta shiga gasar zakarun Turai.
Tsohon kocin Celtic da Tottenham ya maye gurbin Nuno Espirito Santo a watan Satumba, amma har yanzu bai ci wasa ba.
Ya fara da shan kashi 3-0 a gidan Arsenal, sannan Swansea ta yi waje da su daga Carabao Cup da yin canjaras a Burnley da kuma a Real Betis a Europa League na farko a bana.
Sannan kuma Sunderland ta doke ta har gida 1-0 a Premier League a makon jiya.
Tottenham ta kori Postecoglou kwana 16 da ya lashe Europa League.
