Cutar kyanda: Gwamnatin Zamfara za ta gudanar da rigakafi a garuruwa 10,000

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara za ta gudanar da gangamin allurar rigakafin cutar kyanda a garuruwa sama da “10,000” a ƙoƙarin ta na fara aikin haɗin gwiwa da hukumar UNICEF don yaƙi da cutar kyanda, Rubella da Polio a faɗin jihar.

Sakataren zartarwa na hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar, Dakta Hussaini Yakubu Anka ne ya bayyana hakan yayin wani taro da kafafen yaɗa labarai da masu shafukan sada zumunta da U-Reporters da aka gudanar a farfajiyar EOC( Emergency Operations Centre) da ke Gusau ranar Asabar.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar ce ta shirya taron tattaunawar da kafafen yada labarai tare da haɗin gwiwa da hukumar UNICEF.

A cewarsa, rigakafin za a cigaba da aiwatar dashi ko yaushe a cibiyoyin kiwon lafiya na sakandare 23, manyan cibiyoyin kiwon lafiya biyu da cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko guda 724 a faɗin ƙananan hukumomi 14 dake jihar.

Ya ce tuni aka horas da ma’aikata domin gudanar da rigakafin ta hanyar haɗin gwiwa da ƙungiyoyin raya ƙasa irin su UNICEF, don tabbatar da cewa an ba da kulawar rigakafi ga duk ‘yan ƙasa kan cutar kyanda- Rubella da cutar shan inna.

Ya kuma bayyana cewa, akwai buƙatar sarakunan gargajiya, malaman addini da shugabannin al’umma su taka muhimmiyar rawa don samun nasarar rigakafin a faɗin jihar.

Ya ce sama da tawagar ma’aikatan kiwon lafiya 1,280 za a tura domin gudanar da rigakafin a faɗin jihar.

Hakazalika Dr. Anka, ya buƙaci shugabannin addini da na gargajiya da na al’umma da su wayar da kan jama’a muhimmancin rigakafin a jihar.

Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su wayar da kan jama’a kan muhimmancin rigakafin a jihar.

By ukarofi