Gwamnonin Arewa na da kuɗin ɗaukar nauyin tsaro – Gwamna Sule

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya ce, yanzu gwamnatocin jihohi a Nijeriya su na da wadatattun kuɗaɗe fiye da yadda suke da su a shekarun baya.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa wajibi ne a karkatar da kuɗin zuwa sassan da za su iya sauya tattalin arzikin ƙasar nan.

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron Northern Nigeria Inɓestment and Industrialisation Summit (NNIIS) 2025 da aka gudanar a Abuja.

Ya ce, kuɗin da ake rabawa tsakanin matakai uku na gwamnati sun ninka sau huɗu sakamakon gyare-gyaren da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar.

“A karon farko cikin tarihinmu, dukkan matakan gwamnati suna samun kuɗi fiye da yadda suka taɓa tsammani.”

“Sama da Naira tiriliyan 2.2 aka raba a wannan watan kaɗai. Lokacin da na zama gwamna a 2019, muna raba tsakanin biliyan 590 zuwa biliyan 620. Yau kuwa, adadin ya ninka sau huɗu,” inji Gwamna Sule.

Yayin da ya ke ƙara bayani a wajen taron, gwamnan ya ce Nasarawa ta yi amfani da gyare-gyaren da aka yi wajen tilastawa masu saka jari a sashen ma’adanai su kafa masana’antar sarrafa ma’adanai.

Gwamna Sule ya ce, lamarin ya kai ga ƙaddamar da masana’antar da ke sarrafa tan 3,000 a kowace rana, tare da kammala wata babbar masana’antar da za ta sarrafa tan 6,000 a rana wacce ake jiran a ƙaddamarwa.

Haka kuma ya tabbatar da kasancewar filayen mai a jihar da ake hasashen suna ɗauke da aƙalla gangar mai miliyan biyar zuwa bakwai.

Sannan ya bayyana shirin faɗaɗa gonakin shinkafa daga hekta 3,300 zuwa akalla hekta 8,000 kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa.

Gwamna Sule ya shawarci gwamnonin Arewa da su maida hankali kan abin da kowace jiha ta fi kwarewa a kai, su ɗauki alhakin tsaron jihohinsu, kuma su guji dora laifi a kan wasu.

Ya ce, “yanzu kowace jiha na da kuɗin da za ta iya kare mutanenta. Ya kamata mu daina zargin wani game da tsaro. Idan akwai wanda za a zarga, to kanmu za mu zarga.”

By ukarofi