Daga JOHN WADA a Keffi
Shugabar Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman, ta bayyana buƙatar ƙasashen duniya su rungumi sabbin hanyoyin ci gaba da ba wai kawai suna kawo riba ba, amma suna ɗorewa, domin fuskantar manyan ƙalubale irin su sauyin yanayi, ƙarancin abinci, da raguwar albarkatun ƙasa da ke addabar ƙasashe daban-daban na duniya.
Farfesar ta bayyana haka ne a wajen buɗe taron kwana uku na farko na ƙasa da ƙasa kan ƙirƙire Ƙirƙire da nuna kayayyaki , wanda sashen nazarin kasuwanci (Entrepreneurship Studies) na jami’ar ya shirya.
Taken taron shi ne: “Kirkire-Kirkire a Kasuwanci da Ci Gaban Ɗorewa: Tsara Makomar Tattalin Arzikin Duniya.”
A yayin taron, Shugabar Jami’ar ta bayyana cewa jami’ar tana da hangen nesa na gina ɗalibai da malamai masu fasaha, jajircewa da kasuwancin da ke haɗa kowa da kowa, tana mai cewa jami’a ba wai wurin koyon karatu kawai ba ce, har ila yau cibiyar ƙirƙire ƙirƙire ce da haɗin gwiwar masana’antu, tare da sauya burin matasa zuwa ayyukan da za su haifar da riba.
Ta ƙara da cewa tun bayan hawanta kan karagar shugabanci, jami’ar ta ba da fifiko ga ƙirƙire ƙirƙire da haɗin kai da al’umma domin tabbatar da ɗorewar kasuwanci, yayin da ɗalibai a faɗin duniya ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki na zamani.
Farfesar ta ce:
“Tun lokacin da na hau kujerar shugabanci, na shimfiɗa tsari mai ƙarfi na sabuntawa domin dawo da jami’ar mu cikin manyan jami’o’i na duniya masu gudanar da bincike, ƙirƙire ƙirƙire, da haɗin kai da al’umma.
Muna daidaita tsarin karatun mu da bukatun ƙarni na 21, muna sabunta kayayyakin more rayuwa, muna ƙarfafa al’adun bincike da ƙirƙire ƙirƙire, tare da bunƙasa haɗin kai tsakanin jami’a, masana’antu, gwamnati da ƙungiyoyin farar hula.”
A nasu ɓangaren, Masu jawabi na musamman, Dr. Martyna Wronka-Pospiech daga Poland*, da Suleiman Abubakar, daraktan tsare-tsare na Imani sun buƙaci masana’antu, malamai, ɗalibai da masu ƙirƙire ƙirƙire su haɗa kai wajen sake fasalta kasuwanci domin ci gaban duniya.
Sun kuma ƙarfafa sabbin ‘yan kasuwa a faɗin duniya su yi amfani da irin wannan dandali wajen ƙarfafa yanke shawarar kasuwanci da cigaban tattalin arziki a ƙasashen su.
A nasa jawabin, Dekan Fakultin Gudanarwa, Farfesa Abdullahi Zubairu, ya bayyana cewa wannan taro na farko na ƙasa da ƙasa ya samar da dandali ga masana da masu ƙirƙire ƙirƙire domin musayar ra’ayoyi, dabaru da mafita fiye da iyakokin ƙasa.
Ya yaba wa sashen nazarin kasuwanci bisa shirya wannan taro na farko na ƙasa da ƙasa kan ƙirƙire ƙirƙire da nuna kayayyaki, tare da buƙatar mahalarta su yi musayar ilimi domin samar da tattalin arziki mai ɗorewa, haƙiƙa da haɗin kai.
Ya ce:”Masu kasuwanci da masu gudanarwa dole su rungumi ƙirƙira, juriya, da ɗaukar alhaki domin gina mafita da ba wai kawai za su bunƙasa tattalin arziki ba, har ma za su kare makomar ‘ya’yanmu.”
Shi kuma shugaban kwamitin shirya taron, Dr. Vincent Paul, ya jaddada cewa kasuwanci na gaskiya a yau ya kamata ya wuce samun riba kawai, ya rungumi ɗorewa, haɗin kai da ƙirƙira domin magance matsalolin al’umma.
Ya ce “Wannan taro ya haɗa manyan masana, ‘yan kasuwa, shugabannin masana’antu da ɗalibai domin musayar bincike, nuna sabbin kayayyaki da kuma tattauna ra’ayoyin da za su iya tsara makomar tattalin arzikinmu da al’ummarmu.”
Ya gode wa Shugabar jami’ar da sauran shugabannin saboda goyon bayan su, ya kuma yaba da jajircewar mambobin kwamitin da kuma mahalarta.
Ya ƙara da cewa: “Na gode wa shugabar sashen kasuwanci da ta ba ni da kwamitina wannan amincewa domin kafa sabon tarihi a sashenmu.”
A.T.P News ta ruwaito cewa Sarakunan gargajiya da manyan baƙi da suka halarci taron sun haɗa da sarkin Keffi, Dr. Muhammed Chindo Yamusa da Abaga Toni, Mai Martaba Lawrence Ayih, tsohon Shugaban Jami’ar Farfesa Mohammed Mainoma da shugabannin sassa daban-daban.
