NFF ta dakatar da alƙalan wasan da su ka busa wasan Kano Pillars da Shooting Stars

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kwamitin alƙali wasa na hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa NFF ta dakatar da alƙalan wasa guda uku da suka busa wasan Kano Pillars da Shooting Stars na gasar firimiya ta ƙasa, NPFL, wanda aka tashi 1-1 a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar Kano.

An dakatar da su ɗin ne bisa gaza bin ƙa’idojin busa na ƙasa a wasan na mako na 8, lamarin da ya haifar da rikici bayan an tashi daga wasan.

A sanarwar da sakataren kwamitin, Aminu Muhammad, ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai , NFF ta dakatar da Mohammed B Tuta ɗan asalin jihar Adamawa da nataimakin sa Ben Japhet na jihar Benue, sakamakon yadda suka gudanar da wasan Kano Pillars da Shooting Stars bisa karya ƙa’idojin busa.

Kazalika, a ɓangare guda kuma, hukumar ta ladabtar da Ikechukwu Taiwo ɗan asalin jihar Ribas da ya jagoranci wasan Nassarawa United da Enugu Rangers, sakamakon bada bugun daga kai sai mai tsaron gida na bogi da bai cancanta ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa dukkanin alƙalan wasan an dakatar da su har sai abinda hali ya yi.

By ukarofi