Daga MUHAMMAD ABUBAKAR TAHIR
Jihar Jigawa cikin ƴan shekaru nan na samun yabo wajen tsarin bada aiki ga ɗaliban da suka kammala jami’a da mataki mafi daraja ta ɗaya.
Wannan tsarin abun a yaba ne wanda hakan ke nuni da ƙoƙari Gwamnatin Jihar wajen cigaba ilimi da kuma gina goben matasa domin cigaban al’ummar jihar.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba wajen ɗaukar matasan aiki kai tsaye, shine kamata gwamnati ta yi duba na tsanaki ga ɗaliban da sukayi matuƙar ƙoƙari, amma ƙaddara ta hana su kammala jami’a da mataki mafi daraja na ɗaya, musamman waɗanda suka kammala da CGPA daga 4.0 zuwa 4.49.
Waɗannan haziƙan ɗaliban a zahiri sun kammala da digiri mai daraja ta biyu 2.1, amma duk wanda ya yi jami’a ya san duk wanda ka gani da irin wannan sakamakon ya cancanci a ba shi dama irin ta mai ‘First Class’. Wasu ma daga cikinsu sunfi masu ‘First Class’ ɗin ƙoƙari kawai ƙaddara ce ta saka haka ta faru da su.
Wasu daga cikinsu ɗaka samu sun kammala da misali 4.27 bambancinsu da mai 4.5 shine 0.23. za ka same su ba su da tsuntsu ba su kuma da tarko. Zuciyoyinsu cike da ƙunci da damuwa, babu wani shiri kuma daga gwamnati wajen tarbar su tare da ba su dama domin ciyar da jihar gaba.
Manya-manyan jami’o’in duniya suna karrama irin waɗannan ɗaliban wajen ba su damar karo karatu da ba su guraben ayyuka domin sun nuna hazaƙa da jajircewa.
Misali Chevening, da Commonwealth suna ba wa ɗaliban da suka kammala da CGPA 3.5 zuwa sama damar karo Karatu digiri na biyu ko na uku.
Wannan yake nuna cewa, manyan ma’aikatun da jami’o’in a faɗin duniya suna girmama waɗannan daliban domin amfana da tarin iliminsu da basirarsu domin cigaban al’ummarsu.
A kan wannan nake ma Maigirma Gwamna Malam Umar Namadi hannunka mai sanda kan ya faɗaɗa wannan aikin alkairin domin ba wa sauran ɗaliban dama, wanda hakan zai sa a ribatu da baiwarsu wajen ciyar da jihar gaba.
Idan aka gyara tsarin hakan ɗai ba wa irin wadannan ɗaliban dama, su shigo su bayar da tasu gudunmawar da Allah ya hore musu sun kuma san an kula da su an duba kokensu. Gwamnan Jihar Jigawa ɗai zama ta yi adalci ga dukkanin al’ummar jihar wanda suka fito daga mabambanta yankuna na faɗin jihar.
Irin wannnan tsari kwananan Gwamnatin Jihar Kano ta fito da shi wajen ba wa masu 2.1 damar karo karatu a jami’o’i daban-daban da ke faɗin ƙasar nan, inda ake sa ran tsarin ya taimaka wa ɗaliban da yawa da suka fito daga ƙauyuka da birane da ke sassan faɗin jihar, wanda hakan ɗai inganta tare da taimakon dubban al’ummar da su dogara da ’ƴan uwansu da suka samu wannan damar.
A sanina dai gwamnatin Malam Umar Namadi a buɗe take wajen karɓar ƙorafin al’ummar da suka ɗabe shi wanda mun tabbatar da haka lokaci azumi Ramadan inda mukayi kira kan inganta tsari, cikin ƙanƙanin lokaci gwamna ya yi abun da ya dace. Haƙiƙa mun yaba masa kan tsari nasa.
Faɗaɗa irin wannan zai sake kankaro da mutunci Malam Umar Namadi a idon irin waɗannan ɗaliban da ’yan uwansu wanda haka zai sake tabbatar da haƙiƙa gwamnatinsa cike ta ke da adalci da jinƙan al’ummarsa.
Tarihi ba zai taɓa mance Malam Umar Namadi ba idan ya yi duba da wannan kukan, hakan zai ƙara tabbatar da cewa, gwamna shugaba nagari ne wanda yake tafiya da kowa a jiharsa ba tare da nuna bambanci ba, domin a gudu tare a kuma tsira tare, ba kuma da wata hanya da za su isar da wannnan saƙon sai dai ta irin wannan hanyar.
Na bar ka lafiya.
Muhammad Abubakar Tahir ɗan jarida ne da ke zaune a Hadejia ta Jihar Jigawa
