Gwamnatin Katsina ta fara jigilar kayan abinci buhu 90,000 domin daƙile cutar Tamowa

Spread the love

Jigilar abincin, yana gudana ne ƙarƙashin kwamitin da Gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa domin aikin daƙile yaɗuwar cutar yunwa a fadin jihar, wanda Malam Ahmad Musa Filin Samji yake jagoranta.

Tun bayan fitar da wani rahoto, da ƙungiyar “Medicine Sans Frontier” sukayi wanda su ka bada ƙididdigar sama da yara 6000 sun mutu sanadiyar cutar tamowa a Jihar Katsina, Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya kafa wannan kwamiti domin shawo kan wannan matsala.

Bayan kafa kwamitin, Gwamnan ya bada umarnin fitar da abinci buhu 90,000 a raba a ƙananan hukumomin jihar, a matsayin somin taɓi na tsare, tsaren gwamnatin na daƙile yaɗuwar cutar yunwa a jihar.

Buhunan abincin sun haɗa da buhun masara 30,000 , buhun 30,000 , buhun dawa 30,000, kuma yanzu haka ana ci gaba da jigilar abincin zuwa ƙananan hukumomin Jihar Katsina 34.

Ana Jigilar abincin daga wuraren aje abinci na gwamnati na shiyya, ƙananan hukumomin shiyyar Katsina ana jigilar abincin su daga wurin aje abinci na gwamnati da ke Katsina.

Ƙananan hukumomin shiyyar Daura kuma ana jigilar nasu daga wurin aje abinci na gwamnati da ke Daura, yayin da ƙananan hukumomin shiyyar Funtua ake jigilar na su daga wurin aje abinci na gwamnati da ke Funtua.

Jigilar abincin, kamfanin “Alfahari Logistics solution” yake gudanar da aikin jigilar, ya kuma samar da motocin Jigilar masu lafiya, waɗanda ba za a samu wata tangarɗa ba, yayin gudanar da Jigilar.

Kazalika kamfanin ya samar da ma’aikata (Leburori) dake gudanar da aikin cikin natsuwa ba tare da an ɓannatar da kayan ba, ana dorasu lafiya lau, tare da kaisu wuraren da ake kaisu lafiya lau.

By ukarofi