Majalisar Dokokin Zamfara ta amince da ƙudirin kafa kotunan tafi da gidanka

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara za ta amince da ƙudirin kafa ƙananan kotunan tafi da gidanka da domin su fara aiki yadda ya kamata a jihar.

Hon. Rulwan Marafa Anka, mamba mai wakiltar mazabar Anka Kuma shugaban kwamitin koke-koken jama’a yace idan aka kafa kotun, za ta ci gaba da magance cunkoso a fannin shari’a.

Hon. Anka ya bayyana hakan ne a zaman sauraron jama’a wanda hukuma mai zaman kanta, International Alert ta shirya tare da haɗin gwiwar majalisar dokokin jihar da aka gudanar a zauren taro a harabar majalisar dokokin jihar da ke Gusau ranar Alhamis.

A cewarsa, ƙudirin ya sami amincewa a karo na biyu kuma yana ci gaba da tafiya cikin tsarin dokoki, wanda ya haɗa da sake dubawa na kwamiti da kuma zaman sauraron jama’a, da nufin sabunta tsarin shari’a don ya zama mai sauƙi ga ‘yan ƙasa.

A cewarsa, ‘yan majalisar dokokin jihar sun ziyarci jihohi kamar Legas da Kaduna don nazarin tsarin kotunan .

Ya bayyana cewa manufar kafa cibiyar ADR a jihar ita ce samar wa ‘yan ƙasa hanyoyin warware taƙaddama cikin sauri a wajen kotunan gargajiya da kuma inganta zamantakewa.

“Ana sa ran za ta rage wa mutane raɗaɗin da suke fuskanta ta hanyar rage ɗaukan dogon lokaci da kuɗaɗen da ake kashewa a shari’o’in kotuna”. Hon. Anka ya bayyana.

A cewarsa, cibiyar da za a kafa za ta yi ƙoƙarin tabbatar da samun damar yin adalci ga kowa, gami da ƙungiyoyi masu rauni.

“Matsayin da ake ciki da matakai na gaba na aiwatar da dokar yana ci gaba a Majalisar Dokoki saboda haka, bayan kammala karatunta na farko da na biyu kuma a halin yanzu tana matakin kwamiti, inda za a sake duba ta.” Hon. Anka ya yi nuni

Da yake magana, Sarkin Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Zamfara, Alh. Attahiru Ahmad ya bayyana cewa idan kotun ta wanzu, za ta kula da harkokin alummar jihar .

Ya yaba wa ƙungiyoyi masu zaman kansu, musamman International Alert saboda jajircewar su wajen tabbatar da samun adalci tsakanin ‘yan ƙasa a jihar.

A cikin jawabinsa, Sunday Momoh Jimoh, Manajan Ayyuka na International Alert Nigeria a Jihar Zamfara, ya bayyana cewa idan aka zartar da ƙudirin dokar, International Alert za ta yi aiki tare da gwamnatin Jihar Zamfara da cibiyoyin da suka dace don tallafawa da aiwatar da cibiyar ADR yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa International Alert za ta gina ƙarfin ma’aikatan cibiyar don samar musu da ilimi da ƙwarewa a fannin sulhu, gudanar da shari’o’i, da kuma ƙa’idojin Shari’a.

“Za mu tallafa wa manyan ma’aikatu, sassa, da hukumomi don samar da hanyoyin aiki na yau da kullun (SOPs) waɗanda za su jagoranci ingantattun hanyoyin isar da ƙararraki da kuma daidaita su”. Ya ƙara da cewa.

Ya tabbatar da cewa International Alert za ta tallafa wajen samun damar koyon harkokin Shari’a don tabbatar da cewa tsarin ADR a Zamfara ya dace da mafi kyawun ayyuka na ƙasa da ƙasa wajen samun adalci da gina zaman lafiya.

By ukarofi